An kalubalanci iyaye kan ilimin ’ya’yansu
An kalubalnnci iyaye su sauke nauyin da Allah Ya dora musu na tabbatar da ganin ’ya’yansu sun sami ilimin addini da na zamani don samun rayuwa tagari.Sarkin Fulanin Legas, Alhaji Muhammadu Abubakar Bambado shi ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da Aminiya a wurin taron yaye daliban makarantar Islamiyya ta Alfaidiyya da aka […]
An kalubalnnci iyaye su sauke nauyin da Allah Ya dora musu na tabbatar da ganin ’ya’yansu sun sami ilimin addini da na zamani don samun rayuwa tagari.
Sarkin Fulanin Legas, Alhaji Muhammadu Abubakar Bambado shi ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da Aminiya a wurin taron yaye daliban makarantar Islamiyya ta Alfaidiyya da aka gudanar a Legas a karshen makon da ya gabata.
Ya ce “Ya zama wajibi iyaye su gane cewa ba wa ’ya’yansu ilimin adddini da na boko wani nauyi ne da Allah Ya dora musu, wanda ya zama farilla su sauke shi. Babu gatan da za ka iya yi wa danka da ya wuce ka ba shi ilimi a rayuwa domin shi ne gishirin zaman duniya. Babu shakka abin alherin da wadanda suka gina makarantar suka kafa abin a yi koyi da shi ne domin abu ne da za a rika cin gajiyarsa har a nade kasa”.
Ya ci gaba da cewa, “Baya ga ilimi sai tarbiyya, wacce ita ma hakki ne na iyaye da Allah Ya dora musu. Saboda haka nake kira ga iyaye su dage wajen ganin ’ya’yansu sun sami tarbiyya tagari don yin rayuwa mai kyau”.
Da yake jawabi, sarkin Hausawan Agege, Alhaji Muhammdu Dogon Kadai, ya shawarci matasa su kasance masu ladabi da biyayya ga manya. “Mu an koya mana ladabi da biyayya ga manya, don idan babu ladabi da biyayya, babu yadda za a samu alheri da albarkar manya. Ya kamata matasa su dage kada su bari a bar su a baya wajen neman ilimin boko da na addini domin su ne gishirin zaman duniya”. Inji shi.
Makarantar Alfaidiyya ta yaye dalibanta 52, wadanda suka kammala karatunsu a matakai daban-daban.
Da yake magana a madadin kwamitin tsofaffin daliban makarantar, Alhaji Sani Pikin ya yaba da kwazon da yaran suka nuna a makarantar.
Ya ba da tabbacin cewa kwamitin nasu zai ci gaba da tallafa wa makarantar har sai ta cimma burin da ta sa a gaba.