An kama ƙasurguman masu garkuwa da mutane 33 a Nasarawa

Cikin ababen zargin har da waɗanda suka yi garkuwa da wasu ɗaliban Jami’ar Tarayya ta Lafiya.

An kama ƙasurguman masu garkuwa da mutane 33 a Nasarawa

Rundunar ‘yan sanda ta ce ta kama wasu ƙasurguman masu garkuwa da mutane 33 da suka addabi sassa daban-daban a Jihar Nasarawa.

Cikin wadanda aka kama har da waɗanda suka yi garkuwa da wasu ɗaliban Jami’ar Tarayya ta Lafiya da ke Unguwar Gandu a yankin Mararaba a jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Shehu Umar Nadada a yayin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a hedikwatar rundunar a ranar Alhamis a Lafiya ya bayyana cewa, an kama dukkan waɗanda ake zargin ne a maɓoyarsu daban-daban.

Ya ce, “Waɗanda aka kama su 13 ne da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, 11 da ake zargin ’yan fashi da makami ne, ɗaya da ake zargin ɓarawon shanu ne da kuma waɗanda ake zargi da aikata fyaɗe biyar, ciki har da wasu mutane biyu da ake zargin su zamba.

A cewarsa, “A ranar 4 ga Afrilu 2024, an samu labarin cewa an yi garkuwa da mutane huɗu a Rukubi, kuma an tura sashin yaƙi da garkuwa da mutane na rundunar don bin diddigin waɗanda ake zargin tare da kuɓutar da waɗanda abin ya shafa.

“Bayan nasarar da aka samu tare da ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su, yayin da aka kai su garin Rukubi, waɗanda abin ya shafa sun ga ɗaya daga cikin waɗanda suka yi garkuwa da su mai suna Shagari Ibrahim na garin Kadarko, Ƙaramar Hukumar Keana, inda nan take aka kama shi.

“Da aka yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa laifinsa ga Hukumar da aikata laifin.

“Sannan ya ƙara da ɗaukar alhakin sace wasu ɗaliban Jami’ar Tarayya ta Lafiya a Otal ɗin Confidence da ke kan titin Makurdi, zuwa Lafiya.

“Daga nan ya amsa cewa ya gudanar da ayyukan garkuwa da mutane a Rukubi da Gandu da Kadarko da Agyaragu.

“A ranar 14 ga Afrilu 2024 da misalin ƙarfe 3:00 na rana, bisa samun sahihan bayanai, jami’an ‘yan sanda da ke ofishin ‘B’ Division, Lafiya sun kama wani Umar Idris mai unguwar Rukubi a Ƙaramar Hukumar Doma bisa zargin satar shanu inda aka samu kuɗi miliyan ɗaya da ɗari uku da dubu talatin a hannunsa.

“Wanda ake zargin ya amsa laifin satar shanu yana mai cewa ita ce babbar hanyarsa ta samun kuɗi; an kama shi ne a gidan karuwai a lokacin da yake jin daɗin aikata laifin.”