An kama ƙasurgumin ɗan ta’adda a Yobe
Rundunar ta jima yana bin diddigin ɗan ta’addar kafin daga bisani ya shiga hannunta.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ta sanar da kama ƙasurgumin ɗan ta’adda, Haruna Mohammed mai shekara 40.
Kakakin rundunar, Mista Dungus Abdulkarim ne, ya shaida wa manema labarai cewa, hukumar leƙen asiri ta jihar (SID) ce ta kama wanda ake zargin.
- Sojoji ku kokarta ’yantar da al’umma daga mahara —Shehun Borno
- DAGA LARABA: Yadda Kanawa Suka Je Kallon Hawan Daushe A Zazzau
“Yana hannu wajen kai hare-hare garuruwa, ƙauyuka da jihohin da ke maƙwabtaka Yobe ta hanyar kiran mutane a waya, da neman kuɗi da kayayyaki masu daraja daga hannun waɗanda ya kama.
“Rundunar ta jima tana bin diddigin Mohammed ne saboda laifukan da ya aikata.
“Wani mutum daga ƙauyen Simnti, ya bayyana cewar Mohammed ya buƙaci Naira miliyan a hannunsa ko kuma ya kashe shi tare da iyalinsa.
“A wani samamen sirri da aka kai a ranar 16 ga watan Yuni, jami’an tsaron SID sun kama Mohammed a ƙauyen Nagillam da ke ƙaramar hukumar Tarmuwa.
“Wanda ake zargin ya amsa laifukan da ake zarginsa da aikatawa, ya kuma bayyana sunayen wasu ‘yan ƙungiyarsa da ake nema ruwa a jallo a jihar,” in ji shi.