An kama ɓarayin waya a Kano

’Yan sanda sun ce akan samu miyagu da suke sojan gona a matsayin masu sayen kayayyaki a kasuwa.

An kama ɓarayin waya a Kano

Rundunar ’yan sandan Kano ta cafke wasu matasa biyu kan zargin satar wayoyin hannu a kasuwar waya ta Beirut da ke birnin na Dabo.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce an cafke ɗaya daga cikin ababen zargin ne yana yunƙurin satar waya a wani shago.

Sai dai kakakin ’yan sandan ya ce wani abokin ɓarawon da suka yi yunƙurin aika-aikar tare ya tsere da wayar da suka sata.

SP Kiyawa ya ce bayan binciken da aka gudanar ne ’yan sanda suka cafke wani mai suna Abduljabbar Musa Sheka kan zargin sayen wayoyin hannu da aka sata.

Ya ƙara da cewa za a gurfanar da ababen zargin a gaban kuliya da zarar sun kammala bincike.

Rundunar ta gargaɗi ’yan kasuwa da su zama masu lura da abokan hulɗar da suke mu’amala da su, yana mai cewa akan samu miyagu da suke sojan gona a matsayin masu sayen kayayyaki a kasuwa.

Kazalika, rundunar ta yi kira ga duk wani ɗan kasuwa da irin haka ta faru da shi da ya gaggauta kai rahoto ofishin ’yan sanda mafi kusa.

’Yan bindiga sun hallaka mutum 6 a ƙauyukan Kebbi

Matata ta taɓa kawo min ƙarar Akpabio — Mijin Natasha

Mu ne muka kai samame otal ba ’yan bindiga ba — EFCC

Girke-girken Azumi: Yadda ake yin Tsiren Dankali