An kama ɗalibai masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Amurka

An samu hatsaniya tsakanin masu zanga-zangar nuna goyon baya da kuma masu ƙin jinin Falasɗinawa.

An kama ɗalibai masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Amurka

’Yan sandan a ƙasar Amurka sun kama gomman ɗaliban Jami’ar Columbia yayin zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasɗinawa da ke fuskantar hare-haren Isra’ila.

’Yan sandan dai sun fara kama ɗaliban ne da karfe 9 na daren Talata, suna jefa su cikin motoci, yayin da wasu ɗaliban ke yi wa ’yan sandan ihu.

Shugabar Jami’ar, Minouche Shafik, ta buƙaci ’yan sandan su ci gaba da zama a harabar jami’ar har zuwa ranar 17 ga wannan wata na Mayu, don tabbatar da tsaro da zaman lafiya, a daidai lokacin da ake shirin bikin yaye ɗalibai nan da ’yan kwanaki.

An yi artabu tsakanin ɗalibai masu goyon baya da ƙin jinin Falasɗinawa 

An samu hatsaniya a Jami’ar California da ke Amurka tsakanin masu zanga-zangar nuna goyon baya da kuma masu ƙin jinin Falasɗinawa.

Lamarin ya faru ne lokacin da gungun masu zanga-zangar goyon bayan Isra’ila ne suka rika yin jifa da turakun da aka sanya domin killace masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa.

Bidiyon da aka yaɗa ya nuna yadda ɓangarorin biyu suka riƙa jifan juna da tartsatsin wuta.

Haka nan bidiyon ya nuna yadda aka lakaɗa wa wani mutum sanye da rigar nuna goyon baya ga Falasɗinawa duka.

Daga baya ’yan sanda sun samu shiga tsakanin masu husumar.

Zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasɗinawa na ci gaba da yaɗuwa a jami’o’in Amurka kamar yadda BBC ya ruwaito.

Sama da mutum 1000 ne aka kama cikin mako biyu sanadiyyar zanga-zangar.