An kama ɗan sandan ƙarya a Kano

Yana damfarar jama’a da shigar jami’an ‘yan sandan da kuma lalata martabar Rundunar.

An kama ɗan sandan ƙarya a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama Salisu Bala mai shekara 31, wanda ya daɗe yana karɓar kuɗi tare da addabar jama’a da sunan shi ɗan sanda ne.

A sanarwar da Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce ɗan sandan na bogi mazaunin unguwar Kurna Quarters ne a cikin birnin Kano.

Jami’an ‘yan sanda na musamman da ke Unguwar Koki Quarters a Kano ne suka bi sawu suka kama shi, inda aka gan shi, sanye da baƙar rigar ‘yan sanda mai ɗauke da hular kakin ‘yan sanda.

An ce ya damfari jama’a da ba su ji ba, ba su gani ba inda yake shigar jami’an ‘yan sandan da lalata martabar Rundunar.

Gobarar Tankar mai: Gwamnatin Kano ta ba da gudunmawar N100m ga Jigawa

An kama ɗan sandan ƙarya a Kano

Zargin kwartanci: Hisbah ta kama kwamishina da matar aure a Jigawa

Fashewar tankar mai: Mamata sun ƙaru zuwa 170