An kama ɗan sandan da ya yi wa matashiya fyaɗe a Legas

Ana zargin ɗan sandan ya yi wa matashiyar fyaɗe a ofishinsa.

An kama ɗan sandan da ya yi wa matashiya fyaɗe a Legas

An kama ASP Owolabi, jami’in ɗan sandan da ake zargin ya yi wa wata matashiya mai shekara 17 a duniya fyaɗe a ofishin ’yan sanda na Ojota da ke Jihar Legas.

Ana zargin lamarin ya faru ne a ofishin Owolabi, lamarin da ya sa hukumar kula da cin zarafin mata ta Jihar Legas ta ɗauki matakin gaggawa.

Wasiƙar da aike wa Kwamishinan ’yan sandan jihar, Adegoke Fayoade, ya kai ga kama jami’in tare da fara bincike cikin gaggawa.

Kakakin rundunar jihar, Benjamin Hundein, ya tabbatar da kama jami’in, ya kuma tabbatar wa jama’a cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Kwamishinan ya jadadda aniyar cewar idan aka samu jami’in da laifi zai fuskanci hukunci mai tsauri bisa dokokin ’yan sanda da doka.

Ya sake jaddada wa jama’a jajircewar rundunar na kiyaye dokoki da kuma kare jama’a.

Mahaifiyar yarinyar, Misis Aramide Olupona, ta zargi ‘yan sanda da yunkurin yin rufa-rufa kan lamarin, wanda hakan yake barazana ga lafiyar ’yarta.

Duk da yunƙurin da iyalan jami’in da kwamandan yankin suka yi na warware lamarin cikin masalaha, mahaifiyar yarinyar ta ce sai inda ƙarfinta ya ƙare don ganin an yi wa ’yarta adalci.

Aminiya ta ruwaito cewar lamarin ya faru ne bayan da ɗan sandan ya yi ƙoƙarin taimakon yarinyar wajen gano wayarta da aka sace.

Daga bisani ya yaudare ta zuwa ofishinsa wanda a nan ne ake zargin ya yi mata fyaɗe.

NCC ta amince wa kamfanonin sadarwa ƙara kuɗin kira da data

Amurka jinsin mace da namiji kaɗai ta sani a hukumance — Trump

An rantsar da Donald Trump a matsayin Shugaban Amurka na 47

Za mu yi gwanjon motoci 891 da muka ƙwace — EFCC