An kama alhazan Gombe da tan biyu na goro a bara
Sakataren Hukumar Alhazai ta Jihar Gombe Malam Usman Gurama, ya ce a bara an kama alhazan jihar da goro tan biyu a kan hanyarsu ta zuwa aikin Hajji, kuma sun sha alwashin ganin hakan bai auku a bana ba.Sakataren ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Gombe inda ya ce […]
Sakataren Hukumar Alhazai ta Jihar Gombe Malam Usman Gurama, ya ce a bara an kama alhazan jihar da goro tan biyu a kan hanyarsu ta zuwa aikin Hajji, kuma sun sha alwashin ganin hakan bai auku a bana ba.
Sakataren ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Gombe inda ya ce maniyyatan bana daga Gombe za su fi na bara da’a da bin doka, domin sun fara nuna alamun haka a wajen bitar da ake yi musu.
Ya ce yanzu haka sun fara tantance maniyyatan don gano ko akwai masu dauke da wata cutar da za ta hana su sauke faralin a bana, amma har yanzu babu ko mutum daya da suka samu da wani ciwo kuma ba a samu ko mace daya da take dauke da juna biyu ba.
Malam Gurama, ya ce sun tanadi magunguna don amfanin maniyyatan jihar koda za a samu matsalar rashin lafiya.
Ya ce rashin bin dokar kasar ya sa a bara a filin jirgin sama na jihar aka samu goro mai yawan tan biyu, maniyyatan na shirin zuwa da su Saudiyya.
Ya sharaci maniyyatan jihar su kasance masu bin doka da oda, musamman idan suka tuna sun kashe dukiyarsu ce don sauke farali.
Kimanin maniyyata dubu daya da 980 ne har da jami’an da za su kula da mahajjatan za su sauke farali bana daga Jihar Gombe kuma tuni har an fara yi musu biza.