An kama attajirai masu fama da cutar son sata a Sharjah
Hamshaqan attajirai da suka shahara a birnin Sharjah na fuskantar tuhumar sata a gaban hukuma, bayan da aka kama mafi yawan su suna satar kaya a kantu, a cewar Kanar Dokta Khalifa Kalander Darakta a hukumart ’yan sandan Sharjah, wanda ya dangata al’amari da xabi’ar da ke xamfare a tunatinsu, amma ba rashi ba. Kuma […]
Hamshaqan attajirai da suka shahara a birnin Sharjah na fuskantar tuhumar sata a gaban hukuma, bayan da aka kama mafi yawan su suna satar kaya a kantu, a cewar Kanar Dokta Khalifa Kalander Darakta a hukumart ’yan sandan Sharjah, wanda ya dangata al’amari da xabi’ar da ke xamfare a tunatinsu, amma ba rashi ba. Kuma ya ce suna fama da ciwon son yin sata, al’amarin da masana tavin qwaqwalwa ke yi wa laqabi a turancin kimiyya da “Kleptomanic.”
Kanar Kalandar ya yi misali da wani miliyoniya a cikinmasu kuxin larabawa da aka kama shi, aka kais hi ofishin ’yan sanda a Sharjah, bayan da malamar jinya a asibiti mai zaman kansa t akai qarar cewa ya sace mata wayar hannu, waddda kuxinta bai wuce Dirhami 200 (kimanin Naira dubu 10) ba.
Da hukuma ’yan sanda ta aike wa mutumin sammace sai ya zo a cikin wta zuqeqiyar mota da kuxin suka kai rabin miliya, wato daidai da Naira 25,000,000. Ana tuhumarsa nan take ya yi iqrarin yin satar a gaban ’yan sanda, cewa, ya saci wayar hannu, amma bai san abin da ya ingiza shi ga aikata hakan ba.
Ya qara da cewa ba da niya ya yi ba, amma yana fama da cutar sha’awar yin sata mai tsanani, kuma wannan matsala ta same shi ne tun yana xan qarami. Bayan da ya amsa laifin satar wayar salular a gaban ’yan sanda, sai attajirin ya mayar wa da malamar jinya wayarta, kuma ya biyata diyya.
An dai warware wannan matsala bayan da malamar jinyar tya janye qarar da take yi wa mutumin.