An kama babur 202 na ’yan bindiga a Katsina
Ana amfani da baburan wajen kai wa ’yan bindiga abinci da man fetur.
Babura akalla 202 mallakin ’yan bindiga da masu hada baki da su ne aka kama a Jihar Katsina.
Akasari babura ne kirar Boxer da Jencheng aka kama, kuma an kama su ne a cikin dazukan da ke makwabtaka da iyakar Najeriya.
- Ciyo wa Najeriya bashi zalunci ne da bautar da na baya —Sheikh Nuru Khalid
- Kwastam ta kama buhu 707 na shinkafar waje a Kano
Da yake sanar da kamen a ranar Juma’a, Kwanturolan Hukumar Kwastan a Jihar Katsina, Chedi Wada, ya ce “Muna zargin ana amfani da babura ne wajen yin jigilar man fetur da kayan abinci zuwa maboyar ’yan bindiga a cikin dazukan.
“Yawancin mutanen aka kama da baburan tserewa suka yi suka bar su, kuma har yanzu babu wanda ya zo neman a ba shi babur dinsa’’.
Chedi Wada ya ce an kama baburan ne daga watan Agusta zuwa Satumba, sannan ya jaddada aniyar hukumar ta tabbatar da tsaro da kuma sanya kafar wando da masu yin faskwaurin kayayyaki.
“Yaki da ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane da satar shanu da sauran nau’ikan laifuka a Jihar Katsina da ma Najeriya baki daya yana bukatar a yi masa taron dangi.
“Hukumar kwastam tana da rawar da za ta taka kamar sauran hukumomin tsaro.
“Saboda haka za mu ci gaba da yin duk mai yiwu a nan Jihar Katsina domin karya lagon ayyukan ’yan bindga da sauran masu aikata manyan laifuka,” inji shi.