An kama bama-baman da aka boye a cikin kayan gwangwan a Kaduna

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama wasu bama-bamai da ba su fashe ba da wasu tarin makamai da aka shigar da su jihar cikin kayan gwangwan daga jihar Borno. Lamarin dai ya jefa fargaba a zukatan mutane kan yadda kayayyaki ke yawo babu bincike daga jihohin da ke fama da rikici. Yadda kwacen babur […]

An kama bama-baman da aka boye a cikin kayan gwangwan a Kaduna

Kaduna

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama wasu bama-bamai da ba su fashe ba da wasu tarin makamai da aka shigar da su jihar cikin kayan gwangwan daga jihar Borno.

Lamarin dai ya jefa fargaba a zukatan mutane kan yadda kayayyaki ke yawo babu bincike daga jihohin da ke fama da rikici.

Kakakin rundunar a jihar, DSP Mansir Hassan ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce an kama kayan ne ranar Asabar bayan wasu bayanan sirri da rundunar ta samu.

Ya ce an samu kayan ne a cikin wani kamfanin da ke hada-hadar kayan gwangwan da ke rukunin masana’antu na Kudandan da ke karamar hukumar Kaduna ta Kudu.

“Wasu kwararrun jami’anmu daga sashen da ke kula da abubuwa masu fashewa ne ya je wajen bayan bayanan. Bayan cikakken bincike, an tabbatar da cewa kayan bama-bamai ne da ba su kai ga fashewa ba,” in ji Mansir.

Kakakin ya ce nan take jami’an nasu suka kwashe bama-baman zuwa wajen da ya dace sannan suka lalata su ba tare da sun fashe ba.

Ya kuma ce yayin aikin, dakarun sun gano makamai, cikin har da wata karamar bindiga kirar gida wacce ke makare da albarusai, da ma wasu tarin makaman.

Kakakin ya ce nan take Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Rabiu Muhammad ya bayar da umarnin rufe kamfanin da aka sami kayan domin a samu damar fitar da dukkan makaman ba tare da an bar ragowa ba.

Kwamishinan ya kuma gargadi masu sana’ar ta gwangwan da su daina kawo irin kayayyakin daga yankunan da suke fama da rikici zuwa jihar ta Kaduna.

Ya kuma ce yanzu haka suna ci gaba da bincike domin gano tushen makaman da kuma dalilin shigo da su cikin jihar.