An kama barauniyar jarirai a Kano

Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta kama wata budurwa da ake zargi ta ‘shahara’ wajen satar jarirai. Jami’an hukumar sun yi nasarar kama budurwar ce mai suna Fatima Yahaya mai kimanin shekara 13 lokacin da aka dana mata tarko a gidan suna a Unguwar Gwammaja a karamar Hukumar Dala inda aka zarge ta da satar […]

An kama barauniyar jarirai a Kano
An kama barauniyar jarirai a Kano

Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta kama wata budurwa da ake zargi ta ‘shahara’ wajen satar jarirai.

Jami’an hukumar sun yi nasarar kama budurwar ce mai suna Fatima Yahaya mai kimanin shekara 13 lokacin da aka dana mata tarko a gidan suna a Unguwar Gwammaja a karamar Hukumar Dala inda aka zarge ta da satar jaka dauke da kudi da wayar hannu.
Aminiya ta gano cewa a lokacin da aka kama yarinyar an same ta da jariri dan kimanin shekara daya wanda ta bayyana cewa wai dan ’yar uwarta ne. Sai dai binciken jami’an Hisba ya gano cewa ta sato yaron ne a wani gidan suna a Unguwar Jarkasa a karamar Hukumar Birni.
“Lokacin da ’yan Hisba suka tambaye ta game da jairirn da take dauke da shi ta bayyana cewa ta sato shi ne a gidan wani suna a Jarkasa kafin ta je daya gidan sunan a Unguwar Gwammaja inda aka kama ta,” inji wani jami’in Hisbah.
Wacce ake zargin ta ce ta yaudari mahaifiyar yaron ne ta hanyar neman ta ba ta shi don ta rike mata kafin ta idar da Sallah. “Yayin da ta fuskanci mahaifiyar yaron ta kusa idar da
Sallar sai ta fice daga gidan tare da yaron,” Inji jami’in.
Hukumar Hisba ta je Unguwar Jarkasa inda ta iske mahaifiyar yaron ta fita daga hayyacinta sakamakon sace yaron, yayin da jama’ar unguwar suka bazama neman yaron.
Barista Nabahani Usman, Mataimakin Kwamandan Hisba bangaren ayyuka na musamman ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce wacda ake zargin ta amsa laifin da ake zargin ta.
Ya ce Fatima ta taba sace wasu yara biyu a Unguwar Kawo a karamar Hukumar Nasarawa inda ta sayar da kowannensu a kan Naira dubu 150 ga wani mazaunin unguwar
kofar Kabuga wanda shi ma hukumar Hisbar ta kama shi.
Har ilaa yua Barista Nabahani ya kara da cewa duba da giraman laifin
Ya ce hukumarsu ta mika maganar ga ’yan sanda don ci gaba da bincike.
Yayin da Aminiya ta tuntube Kakakin Rundunar Yan sanda ta Jihar
Kano ASP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da cewa Hukumar Hisba ta mika musu batun, inda suka fara gudanar da bincike.