An kama barayin jaririya don tsafi a Kano
Kotu ta tsare wasu mutum biyar a gidan yari kan zargin satar jariya ’yar kwana takwas domin yin tsafi a Kano
Kotun Shariar Musulunci da ke zamanta a Gama PRP a Jihar Kano ta bayar da umarnin tsare wasu mutane biyar a gidan yari kan yunkurin satar wata jaririya ’yar kwanaki takwas da haihuwa domin yin tsafi da ita.
Mai gabatar da kara Aliyul Abidin ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhuma sun hada baki domin sace jaririyar wacce ake zargin tsafi za a yi tsafi da ita, su kuma za a biya su Naira miliyan 30 a matsayin ladan aikinsu.
- Shugabar karamar hukuma ta rushe gidajen Gala 39 a Yobe
- An kashe dalibi saboda budurwa a Jami’ar FUDMA da ke Katsina
Sai dai maza biyu daga cikin wadanda ake zargi sun musanta laifukan, a yayin da sauran ukun da ake zargi kuma suka amsa laifin.
Alkalin kotun Mai sharia Nura Yusuf Ahmad ya bayar da umarnin tsare dukkansu, maza hudu da mace daya a gidan gyaran hali tare da dage shari’ar zuwa ranar 26 ga watan Oktoba, 2023.