An kama barayin man taransufoma 2 a Yobe
Rundunar za ta mika su kotu da zarar ta kammala bincike.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ta cafke wasu mutum biyu da ake zargi da satar man dizal din taransufoma a Karamar Hukumar Jakusko a jihar.
Kakakin rundunar jihar, DSP Dungus Abdulkareem ne, ya shaida wa manema labarai hakan.
- ‘Yan bindiga sun yi barazanar kashe mutanen da suka sace a Abuja
- Yadda Tsadar Rayuwa Ta Sa Aka Koma Hawa Jaki A Arewa, Kudu Kuma Tafiyar Ƙafa
Ya ce, rundunar tare da ‘yan banga karkashin jagorancin ASP Lukman Usman, yayin wani aiki sun kama mutanen biyu dauke da man dizel na taransufoma a kan hanyar Jakusko zuwa Gololo.
Ya ce wadanda ake zargin, mazauna Kananan Hukumomin Numan ta Jihar Adamawa da Gamawa ta Jihar Bauchi, an kama su da jarka takwas ta man dizal.
Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun amsa laifin da ake tuhumar su da shi.
Kazalika, kakakin ya ce rundunar za ta mika su kotu da zarar ta kammala bincike a kan su.