An kama boka mai lalata da ’ya’yansa a Ibadan
‘Yan sanda a Jihar Oyo sun kama wani boka mai shekaru 58, Tajudeen Awoniyi, wanda aka zarga da yi wa kananan ’ya’yansa biyu da wasu ’ya’yan dangi guda biyu wanka da bakin sabulun tsafi da ya gusar da hankalisu sannan ya yi lalata da su daya bayan daya. Duka ’yan matan masu shekaru 13 zuwa […]
‘Yan sanda a Jihar Oyo sun kama wani boka mai shekaru 58, Tajudeen Awoniyi, wanda aka zarga da yi wa kananan ’ya’yansa biyu da wasu ’ya’yan dangi guda biyu wanka da bakin sabulun tsafi da ya gusar da hankalisu sannan ya yi lalata da su daya bayan daya.
Duka ’yan matan masu shekaru 13 zuwa 15 sun furta da bakinsu a gaban mahaifin nasu irin dabarun da yake yi kafin ya yi lalata da su. Sun ce a duk lokacin da ya shawo giya sai ya kusance su da yaudara ta hanyar ba su bakin sabulun tsafi da yake yi musu wanka da mika musu wani abu da suke ci a bakinsu wanda hankalinsu yake gushewa sannan ya kama yin lalata da su daya bayan daya.
Asirin bokan ya tonu ne a Juma’ar da ta gabata, lokacin da kanwar matarsa, mahaifiyar biyu daga cikin matan ta dawo daga tafiya, ta fara neman ’ya’yan nata, inda ta gano su a tare da ’ya’yan boka suna gararamba a kan hanya ba tare da sanin inda suka dosa ba. A nan take ta kai rahoto ga ofishin ’yan sanda na Moniya, wadanda suka yi bincike suka gano cewa bokan yana da hannu wajen aikata abun da ake zargi.
Da yake nuna boka sanye da ankwa a hannu da ’yan matan hudu a ofishinsa, Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Oyo, Muhammad Musa Katsina ya ce likitocin Asibitin ‘Yan sanda na Ibadan sun yi bincike, inda suka tabbatar da cewa an yi amfani da al’aurar yaran ta hanyar da ba ta dace ba. Ya ce za su gurfanar da boka ga kotu bayan kammala bincike.
Sai dai Boka Awoniyi ya musanta bayanan da ’yan matan suka yi masa amma ya yarda cewa yana ba su sabulun maganin rigakafin kamuwa da cututtuka. Ya ce a matsayinsa na wanda ya dade yana sana’ar maganin gargajiya, babu yadda za a yi ya aikata wannan al’amari. Ya ce kage aka yi masa domin a bata rayuwarsa.
A wani labara makamancin wannan kuma, a Litinin da ta gabata ce Kwamishina Muhammad Musa Katsina ya jagoranci jami’an sashen yaki da satar mutane zuwa wani gida a cikin kungurmin daji a kauyen Isase, inda ake boye mutanen da aka sato domin neman fansa da buga jabun kudade da kuma tsafe-tsafe. An kama daya daga cikin mutanen da suke amfani da wannan gida mai suna Isma’il Adesina, wanda ya tabbatar da cewa a baya sun boye mutane da aka sato daga sassa daban-daban na kasa a gidan. A cikin gidan akwai wani rami na karkashin kasa da ake cewa aljani yana magana da mutanen da suka kai kansu zuwa gidan domin neman abun duniya. Haka kuma an gano wasu ginannun mutum-mutumi na mutane da dabbobi da manyan rigunan saka da wadannan mutane suke sanyawa a duk lokacin da suka shiga wani kebabben wuri a matsayin zauren taronsu. Har ila yau an gano layu da guraye da ruwan maganin tsafi a cikin kananan kwalabe tare da wasu kananan motoci guda uku da aka kwashe su zuwa hedkwatar ’yan sanda ta Jiha Oyo da ke Ibadan.