An kama budurwa tana kokarin shigar da kwaya kurkuku
Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Jihar Kano ta kama wata budurwa tana kokarin shigar da kwaya cikin kurkukun Kurmawa inda ta cusa kwayar a cikin abinci da niyyar za ta kai wa wani da ke tsare a kurkukun. Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar, Musbahu Lawan Kofar Nasarawa ya shaida wa Aminiya cewa budurwar […]
Budurwar da aka kama za ta shigar da kwaya kurkuku
Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Jihar Kano ta kama wata budurwa tana kokarin shigar da kwaya cikin kurkukun Kurmawa inda ta cusa kwayar a cikin abinci da niyyar za ta kai wa wani da ke tsare a kurkukun.
Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar, Musbahu Lawan Kofar Nasarawa ya shaida wa Aminiya cewa budurwar mai suna Zainab Yusuf mai kimanin shekara 20 tana zaune ne a Unguwar Hotoro a Karamar Hukumar Nasarawa, kuma an kama ta ce lokacin da ake gudanar da binciken masu shige-da-fice da aka saba, inda aka gano ta sanya jaka guda ta kwaya a cikin miya.
A cewar Misbahu Kofar Nassarawa nau’in kwayar da aka kama budurwar da ita, ita ce Diazepam wadda kudinta ya kai Naira dubu 300.
Sai dai Zainab Yusuf ta ce ba ta da masaniyar abin da ke cikin abincin aiko ta aka yi da sako ta kai wa wani da ke tsare a gidan kurkukun, “Ni ban san bin da aka zuba a cikin abincin ba. Ina dawowa daga makaranta aka ba ni in kawo sako nan kurkukun.”
Malam Ibrahim Idris shi ne Shugaban Kurkukun na Kurmawa ya ce da an samu nasarar shigar da wannan kwaya cikin kurkukun Allah ne kadai Ya san irin barnar da za ta haifar wa wadanda ke tsare a kurkukun ta fuskar lafiyarsu da hankalinsu.
A jawabin Shugaban Hukumar Kula da Gidaje Yari ta Jihar Kano Alhaji Magaji Ahmed Abdullah ya bayyana farin cikinsa kan kama wannan kwaya da aka yi inda ya shawarci jami’an hukumar su ribanya kokarinsu wajen ganin sun raba kurkukun da duk wani abu da bai dace ba.
Tuni dai aka mika budurwar ga Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) don zurfafa bincike.