An kama da da uba suna sayar wa dalibai miyagun kwayoyi

Asirin wani magidanci da dansa ya tonu a Legas, lokacin da ’yan sanda suka kama su bisa tuhumar sayar wa dalibai ’yan firamare da ’yan sakandare miyagun kwayoyi na Taramadol da sauransu. Magidanci mai suna Ibrahim Shehu, mai shekara 40 da dansa Faruk Ibrahim, dan shekara 23, an kama su ne a ranar Juma’ar da […]

An kama da da uba suna sayar wa dalibai miyagun kwayoyi


Asirin wani magidanci da dansa ya tonu a Legas, lokacin da ’yan sanda suka kama su bisa tuhumar sayar wa dalibai ’yan firamare da ’yan sakandare miyagun kwayoyi na Taramadol da sauransu.

Magidanci mai suna Ibrahim Shehu, mai shekara 40 da dansa Faruk Ibrahim, dan shekara 23, an kama su ne a ranar Juma’ar da ta gabata, sakamakon korafin da Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Legas ta kai ga ’yan sanda kan wannan barna da ake zarginsu da aikatawa.

Looacin da Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Legas, Imohimi Edgal, yake baje kolin wadanda ake zargin ga ’yan jarida, ya ce sun samu nasarar kama mutanen ne sakamakon korafin da Ma’aikatar Al’amuran Mata ta Jihar Legas ta sanar, cewa suna zargin cewa akwai dalibai a makarantun firamare da sakandare da ake zargin suna tu’ammali da miyagun kwayoyi. Ya ce tare da hadin kan ma’aikatar ne ’yan sanda suka gano makarantar da kuma daliban da ake zargi.

Ya ce bayanan da aka samu daga daliban ne suka taimaka aka samu nasarar kama dillalan kwayoyin da ake zargi da sayar wa daliban Taramadol da sauransu. “Wadanda ake zargin sun amsa laifinsu, cewa suna sayar wa dalibai miyagun kwayoyi. Ina ba iyayen yara shawarar su kula da tarbiyyar ’ya’yansu kuma su lura da abokan huldarsu. Iyaye su rika bincikar ’ya’yansu a kai-a kai bisa abin da suke aikatawa, sannan su rika lura da canjin yanayinsu da halayyarsu,” inji Kwamishinan.

Ya ce, “Haka su ma hukumomin makarantu, ya dace su rika sanya ido game da abubuwan da dalibai suke aikatawa kuma su rika kai rahoton duk wani bako da suka gani yana rabe-rabe a harabar makarantunsu ga jami’an tsaro da ke kusa da su.”

A yayin bincike, an samu kwayoyin maganin Taramadol guda 72 da wasu magungunan na daban daga hannun mutanen da ake tuhuma.

Shi dai Ibrahim Shehu, da farko ya musanta batun sayar da kwayoyin ga daliban, inda ya ce dansa ne ke yin harkar, a duk lokacin da ya ga ba ya kusa. Amma daga bisani ya dawo ya amsa cewa lallai shi ne ke sayarwa tare da dan nasa, inda kuma ya kara da cewa ba dalibai kadai suke sayar ma wa ba, wani lokacin har da sauran mutanen gari.