An kama dagaci saboda yi wa mai kusumbi ciki
Jama’ar garin Dankala da ke gundumar kauran Wali a karamar Hukumar Kudan da ke Jihar Kaduna sun yi wa dagacinsu mai suna Haruna Ahmad ature tare da ihu bisa zarginsa da ake yi na yi wa wata mace mai kusumbi (an sakaya sunanta) ciki har ta haifi da namiji.A ranar Alhamis da ta gabata ne […]
Jama’ar garin Dankala da ke gundumar kauran Wali a karamar Hukumar Kudan da ke Jihar Kaduna sun yi wa dagacinsu mai suna Haruna Ahmad ature tare da ihu bisa zarginsa da ake yi na yi wa wata mace mai kusumbi (an sakaya sunanta) ciki har ta haifi da namiji.
A ranar Alhamis da ta gabata ne mutanen suka yi wa maigarinsu bore tare da jifarsa da yi masa ihu inda suka raka shi har zuwa gidan Hakimin kauran Wali wanda shi ne ya nada shi dagacin tare da matar mai kusumbi wanda ake zargin ya yi mata ciki.
Aminiya ta ziyarci kauran Wali domin gani da jin abin da ya faru a tsakanin talakawa da dagacin nasu, inda Hakimin kauran Wali Alhaji Namadi ya bayyana wa wakilinmu cewa ganin yanayin da al’amarin yake don haka ya tattra su gaba daya ya kai su ofishin ’yan sanda da ke Kudan domin su ne kawai za su iya bincikawa su gane gaskiyar lamarin. “Kuma a mtsayina na Hakimi na sa an rubuta takarda na tura wa Majalisar Sarkin Zazzau a sanar da su abin da yake faruwa don haka iya abin da zan iya cewa ke nan.
Aminiya ta tattauna da wasu daga cikin talakawan garin Dankala wadanda suka nemin a sakaya sunansu, inda suka ce, “Mun dade muna zargin dagacin namu da irin wannan shegantaka da lalata da matan mutane tare da bata kananan yara masu talla, wannan Maikusumbi Bafulatana ce mai tallar nono kuma idan ka gan ta kusumbin ya tauye gaba da bayanta, amma duk da haka sai da ya matsa ya yi ta lalata da ita har ya yi mata ciki ga shi asirinsa ya tonu tunda har ta haifi da namiji kasancewar ya fitine mu ne ka ga jama’a sun taru domin su yi masa bore,” inji daya daga cikin mutanen kauyen.
Wata majiya ta kusa da wanda aka yi wa cikin ta shaida wa wakilinmu cewa tun lokacin da cikin yake da wata uku Maikusumbin ta sanar da Dagaci Haruna Ahmad cewa tana dauke da cikinsa na wata uku amma sai aka ce ya ce mata kada ta damu ai su ne masu gari ba abin da za a yi. Haka aka yi ta tafiya har zuwa lokacin da ta haifi namiji.
An mika Dagaci Haruna Ahmad da Maikusumbi da dan da ta haifa ga Babban Ofishin ’Yan sanda Shiyya ta daya domin ci gaba da bincike.
Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda da ke kula da ofishin da ke Zariya, AC Muahmmadu D. Shehu ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce suna gudanar da bincike kafin daukar matakin da ya dace a gaba.