An kama daliban jami’a bisa zargin kwace mota a Abuja

Shashin tsaro na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya yi nasara kama wasu mutum hudu da ake zargin sun shahara wajen kwace wa mutane motoci wadanda suka hada da daliban jami’ar biyu. Da yake gabatar da mutanen da ake zargi da amfani da makami don kwace motocin, wani babban jami’i a sashin tsaro na […]

An kama daliban jami’a bisa zargin kwace mota a Abuja
An kama daliban jami’a bisa zargin kwace mota a Abuja

Daliban da ake zargi da satar mota tare da motar da suka kwace a AbujaShashin tsaro na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya yi nasara kama wasu mutum hudu da ake zargin sun shahara wajen kwace wa mutane motoci wadanda suka hada da daliban jami’ar biyu.
Da yake gabatar da mutanen da ake zargi da amfani da makami don kwace motocin, wani babban jami’i a sashin tsaro na jami’ar wanda bai so a ambaci sunnansa ba saboda dalilai na tsaro, ya ce biyu daga cikin wadanda ake zargin dalibansu ne, biyu kuma daliban da ke karatun jami’a daga gida ne (National Open Unibersity).
Jami’in ya kara da shaida wa manema labarai cewa daliban hudu da ake zargi sun sato motar ce a garin Jabi da ke Abuja ta hanyar amfani da gatari inda suka sari mai motar kuma suka kwace motar a hannun mai ita a kofar gidansa inda suka nufo garin Zariya domin su sayar.
daya daga cikin daliban mai suna Abdul’aziz Abdulwahid da yake shekara ta biyu a jami’ar a shashin ilimin zamantakewar dan Adam, shi ne wanda ya dauki motar zuwa garin Katsina domin ya sayar saboda sun rasa mai saye a Zariya. Ya ce a sakamakon bayanan asiri da suka samu ya sa suka kai ga nasarar kama wadanda ake zargin.
Jami’in ya ce dalibi na biyu mai suna Abdul A. Abdullahi wanda yake shekara ta hudu a sashin kimiyyar sinadarai ya sa kudi ne domin sayar da motar, su kuma biyun wadanda suka sato motar su ne Arinze Chidindu shi mai shekara biyar a jami’ar NOU kamar yadda bincike ya nuna. Sai shi wanda ya yi amfani da gatari ya sari mai motar mai suna Chukwueduka Mduegbuno.
Ya ce bayan kammala bincikensu da kuma tattara bayannan da suka yi ya tabbatar masu da cewa daliban dukansu sun tabbata masu amfani da makamai don kwace wa jama’a kayansu don haka za su mika su ga ’yan sanda domin su ci gaba da nasu binciken.