An kama dan bindigar Katsina zai kafa sansani a Kano
Dubunsa ta cika bayan ya gudo daga yankin Malumfashi da makamai da kuma dabbobin sata
’Yan sanda sun cafke wani dan bindiga inda suka kwato shanun sata 55 a hannunsa a Karamar Hukumar Karaye ta Jihar Kano.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Usaini Muhammad Gumel, ya bayyana cewa ɗan ta’addan ya tabbatar musu cewa dubunsa ta cika ne a yayin da yake kokarin dawowa jihar Kano da zama.
Dan bindigar, wanda ba a bayyana sunansa ba, ya ce, ya gudo ne daga sansanin ’yan bindiga ta Maidaro ne da ke Malumfashi a Jihar Katsina, ya biyo ta Birnin Gwari a Jihar Kaduna ya shigo Kano.
Ya kuma bayyana cewa ya gudo daga Malumfashi ne sakamakon fadan gungunsu sa na jagoran ’yan bindiga Boderi Isiya.
- Kotu ta sa ranar sauraren rokon daukaka kara kan hukuncin kisan Abduljabbar
- Saurayi ya fille kan budurwarsa a Bayelsa
A cewar dan ta’addan, an kashe jagoran bangarensu da mataimakinsa a fadan, shi ne ya gudo da shanu 55 da tumaki shida da bindigogi uku kirar AK-47, zai koma dajin kananan hukumomin Karaye da Gwarzo na Jihar Kano da zama.
Kwamishinan ’yan sandan ya shaida wa ’yan jarida a ranar Litinin cewa wanda ake zargin ya tabbatar wa ’yan sanda masu bincike cewa an sha zuwa da shi yin garkuwa da mutane a jihohin Katsina da Zamfara da kuma Kaduna.