An kama dan bindiga ya kai hari a masallaci
An cafke wani dan bindiga da ya je zai harbe wa mata a cikin masallaci a watan Ramadan.
Jami’an tsaro sun cafke wani mutum da ya bi wata mata cikin masallaci zai harbe ta tana tsaka da ibada a watan Ramadan.
Matar na cikin masallaci ne ta hango matashin ya tunkaro ta, suna yin ido hudu da shi sai ya fara kokarin zaro bindigar dake jikinsa zai bude mata wuta.
- Juyin mulki: ‘Fadar Shugaban Kasa na cikin rudani’
- ’Yan bindiga sun sako ragowar Daliban Afaka
- Gobara ta lakume rayukan mutum 12 da dukiyar Naira miliyan 17 a Kano
Ita kuma da ganin haka, kan ka ce kwabo, sai ta fita a guje, ba ta tsaya ko’ina ba sai a cikin ofishin ’yan sanda da ke Ebute-Metta, a jihar Legas.
A nan ne ta sanar da su abin da ke faruwa da kuma yadda ta tsallake rijiya da baya a masallacin Ansarudeen da ke unguwar.
Da jin haka, nan take Babban Ofishin ’Yan Sandan na Denton ya tura jam’ai su binciko gaskiyar lamarin da ya faru da misalin karfe 11 na safiyar Litinin.
Da yake tabbatar da labarin, kakakin ’yan sandan Jihar, Muyiwa Adejobi ya ce a yayin samamen ne jami’an suka gano matashin, suka yi masa kofar rago suka tsare shi.
“An kama shi dauke da bindigar ‘Brownie Pistol’ da wayar oba-oba. Ya shaida wa masu bincike cewa ya sayi bindigar ce a kan N80,000 a wurin wani Taiwo, a unguwar Ikorodu a watan Nuwamban 2020.
“Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Legas, Hakeem Odumosu, ya sa a mika shi ga Sashe na Musamman da ke Ikeja domin a kamo sauran mutanen bisa zargin runkurin kashe rai da kuma mallakar makami ba bisa ka’ida ba,” inji shi.