An kama dan Boko Haram a karar shanu ta Ogun
Rundunar ’yan sanda a Jihar Ogun ta yi nasarar kame wani matashi dan shekaru 22 mai suna Mukhtar Umar, wanda ake zargi da kasancewa dan kungiyar Boko Haram.Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Ogun, DSP Olumuyiwa Adejobi ya shaida wa Aminiya cewa rundunar ta kama Mukhtar Umar ne ranar 25 ga watan […]
Rundunar ’yan sanda a Jihar Ogun ta yi nasarar kame wani matashi dan shekaru 22 mai suna Mukhtar Umar, wanda ake zargi da kasancewa dan kungiyar Boko Haram.
Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Ogun, DSP Olumuyiwa Adejobi ya shaida wa Aminiya cewa rundunar ta kama Mukhtar Umar ne ranar 25 ga watan Fabarairun da ya gabata a unguwar karar shanu da ke Mowe a Jihar Ogun.
Ya kuma shaida cewa an kama shi ne da taimakon ’yan Arewa mazauna yankin. Ya kara da cewa tuni dai wanda ake zargin ya amsa tuhumar da ake masa kuma rundunar na ci gaba da bincike don gano iren-irensa da suke buya a Jihar Legas. “Ya gudu ne daga Borno, kimanin shekaru uku da suka gabata. Da fari ya fara zama ne a Isheri, daga bisani ya koma kara, kun san yanzu jami’an tsaro sun yi raga-raga da ’yan kungiyar Boko Haram, shi ya sa suke gudowa nan suna buya, domin an riga an ci karfinsu.”
A lokacin da kwamishinan ’yan sandan jihar, Abulmajid Ali yake gabatar da Mukhtar Umar a gaban manema labarai a ranar Talatar da ta gabata, ya shaida cewa wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumarsa na kasancewa dan Boko Haram, sai dai ya ce a da ne yake dan kungiyar; abin da kwamishinan ya ce ba za a yarda da shi ba, domin dan Boko Haram duk daya ne, da wanda ya yi a da da wanda yake yi a yanzu.
A zantawarmu da wanda ake tuhumar, ya musanta cewa shi dan Boko Haram ne, sai dai ya shaida mini cewa shi dan Maiduguri ne kuma yana da wani aboki mai suna Mustafa, wanda dan Boko Haram, ne suna tare da shi a wani gidan danbe. “To, da ma tare da malaminsu yake sai aka tayar da su, aka rushe inda suke, sai na ce ya zo mu dinga kwana a dakina. Haka muka kasance muna sana’ar wanke mota tare, wata rana sai aka zo aka kashe wani a nan wajen da muke sana’armu sai muka gudu. Bayan da aka kwana biyu muka dawo muka share wajen, muka ci gaba da harkokinmu. To, wani lokacin sai Mustafa ya dade bai zo inda nake ba, wani lokacin sai ya zo na gan shi, daga baya sai na ji an ce dan Boko Haram ne, ana nemansa za a kama shi. Don haka ne yake yin a-sha-ruwan- tsuntsaye, daga baya sai na daina ganinsa gaba daya, bayan wani lokaci ni ma sai aka ce ana nema na a kama. Sai na je na fada wa mahaifina halin da ake ciki, a ranar ban kwana a gida ba sai a gidan wata ’yar uwata. A nan gidanta muka hadu da mahaifina, ya ce na tabbatar ba ni da hannu, na ce masa ni ba ni da masaniya, ni ba dan Boko Haram ba ne. Sai ya ce in yi hakuri in tafi, duk abin da ya faru mai wucewa ne. Tun daga nan ne na taho nan kudu, ina yin sana’ar gwangwan,” inji Mukhtar Umar, wanda ake zargi da kasancewa dan Boko Haram.
Wani wanda ba ya so a bayyana sunansa a unguwar da aka kame wanda ake zargin, ya shaida wa Aminiya cewa wani ne ya gane Mukhtar Umar ya kuma sanar da jama’ar cewa dan Boko Haram ne kuma yana da hannu a kashe wasu ’yan uwansa a Maiduguri. Hakan ne ya sa aka yi hanzarin sanar da jami’an tsaro, wadanda suka kame shi.