An kama dan damfara mai horar da jami’an tsaron bogi

Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa sun yi nasarar kama Amos Samuel wanda yake yi wa kansa lakabi da yana da mukamin Lutanar na sojin sama yana kuma baiwa mabukata shaidar gurbin shiga aikin soja da jami’in dan sanda da dai sauran ayyukan jami’an tsaron farin kaya a jihar. Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar SP Idrisu […]

An kama dan damfara mai horar da jami’an tsaron bogi

Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa sun yi nasarar kama Amos Samuel wanda yake yi wa kansa lakabi da yana da mukamin Lutanar na sojin sama yana kuma baiwa mabukata shaidar gurbin shiga aikin soja da jami’in dan sanda da dai sauran ayyukan jami’an tsaron farin kaya a jihar.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar SP Idrisu Kennedy ne ya bayyana hakan  bayan kama Samuel tare da wasu masu laifi. An dai kama Samuel ne a wani Otal a garin Akwanga dake jihar.

‘Yan sandan sun gano takardun shiga gurbin ayyukan da suka hada da: Hukumar hana fasa kwari (kwastam) sojan sama, sojan kasa da aikin sibil defens da Hukumar shige da fice da Hukumar kiyaye hadurra FRSC tare da amfani da wasu jama’a wajen yin damfara.