An kama dan fashi da matar da ke taimaka musu a Legas
Bangaren ’yan sanda na musamman da ke aikin kai-dauki a karkashin ofishin Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya, (IRT) ya samu nasarar kama wadansu mutu, biyu da ake zargi rikakkun ’yan fashi da makami ne da suka kai farmaki ga masu cirar kudi a na’urar ATM a kan Titin Allen Abenue da yankin Opebi da […]

Bangaren ’yan sanda na musamman da ke aikin kai-dauki a karkashin ofishin Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya, (IRT) ya samu nasarar kama wadansu mutu, biyu da ake zargi rikakkun ’yan fashi da makami ne da suka kai farmaki ga masu cirar kudi a na’urar ATM a kan Titin Allen Abenue da yankin Opebi da ke Legas.
Cikin wadanda aka kama akwai wata mace mai shekara 54 mai suna Basirat Akinmushire da ake zargi da fakewa da sayar da tumatir da tattasai a bakin titi, wadda aka fi sani da Area Mama. ’Yan sanda sun zargi matar da kasancewa mai boye wa ’yan fashin makamansu a karkashin shirginta da ke rukunin gidajen Jakande a Isolo.
Shi kuma dayan mai suna Olatunde Adetunji dan shekara 31 shi ma yana cikin ’yan fashin da ake zargin sun dade suna addabar al’ummar yankin. Wakilinmu ya gano cewa an samu nasarar kama Olatunde ne a yayin da ya jagoranci gungun ’yan fashin don yi wa wata mata ’yar kasuwa da yarinyar da ke mata aiki fashi a kan hanyarsu ta zuwa kai kudi banki a Opebi da ke Ikeja.
Haka kuma ya gano cewa a yayin wannan farmakin mafasan sun kwace miliyoyin Naira daga hannun matar da wayoyi masu tsada, suka arce. Amma bayan kwanaki kadan da faruwar hakan sai ’yan sanda suka yi nasarar kama Olatunde, bayan matar ta gane shi a lokacin da yake kokarin yi wa wani mai amfani da na’urar ATM fashi a kan Titin Toyin da ke Ikeja.
’Yan sandan sun ce Olatunde ya shiga hannu ne bayan da matar ta gaggauta kiran jami’an musamman wadanda suka yi amfani da kwarewa wajen kama mafashin wanda korarren dalibin Jami’ar Legas ne.
An bayyana cewa Olatunde ya amsa laifinsa bayan bincike da tambayoyin da ya fuskanta a karkashin jagoran ayarin ’yan sandan, Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda Abba Kyari wadanda suke aiwatar da ayyukan murkushe fashi da makami da sauran miyagun laifuffuka a birnin Ikko. Abba Kyari ne ya jagoranci ’yan sandan zuwa maboyar wadanda ake zargin, inda aka kama Area Mama da tulin bindigogi da alburusai a shagonta. A yayin hada wannan rahoton ’yan sandan na ci gaba da bincike, kuma sun ce da zarar sun kammala za su mika wadanda ake zargin zuwa kotu don fuskantar hukunci.