An kama dan Najeriya yana safarar Hodar Iblis a Saudiyya
Safarar kwaya dai babban laifi ne a Saudiyya da zai janyo wa mutum daurin shekaru.
Hukumomin Saudiyya sun kama wani dan Najeriya daya da ’yan Saudiyya uku bisa zargin safarar hodar ibilis da ta kai nauyin kilogiram 2.2 a kasar.
Sashen binciken manyan laifuka na rundunar ’yan sandan kasar ya ce ya samu nasarar dakile yunkurin shigar da hodar iblis zuwa biranen Riyadh da Jeddah.
- United na da damar kammala Firimiyar Ingila a sahun ’yan hudun farko — Ten Hag
- ISWAP ta kashe manoma 3, ta sace 11 a Borno
’Yan sandan sun ce mutanen hudu sun dade suna aikata laifin safarar hodar ibilis din tare da sayar da ita a cikin kasar ta hanyar amfani da wasu miyagun dabaru.
Jami’an ’yan sandan sun ce za a gurfanar da mutanen a gaban kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike.
Safarar kwaya dai babban laifi ne a Saudiyya da za a iya yanke wa mutum hukuncin daurin shekaru masu yawa a gidan yari