An kama dan sanda da laifin fyade a Ebonyi(1)

Rundunar ’yan sandan Jihar Ebonyi ta ce tana tsare wani jami’inta da ake zarginsa da yi wa wata yarinya ’yar shekara uku da haihuwa fyade.dan sandan yana aiki ne a karamin ofishinsu na yankin Ugbodo a jihar, a yayin da ya aikata mummunan laifin da ake zargin nasa.Bisa doka, duk wani jami’in gwamnati da aka […]

An kama dan sanda da laifin fyade a Ebonyi(1)
An kama dan sanda da laifin fyade a Ebonyi(1)

Rundunar ’yan sandan Jihar Ebonyi ta ce tana tsare wani jami’inta da ake zarginsa da yi wa wata yarinya ’yar shekara uku da haihuwa fyade.
dan sandan yana aiki ne a karamin ofishinsu na yankin Ugbodo a jihar, a yayin da ya aikata mummunan laifin da ake zargin nasa.
Bisa doka, duk wani jami’in gwamnati da aka samu da zargin aikata laifi irin wannan, ko da kuwa yana sanye da kayan sarki ne, kora ce ka’idar hakan, kamar yadda wakilin Aminiya ya kalato.
 Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Ebonyi, George Okafor, ya ce abin tsiya ma, shi jami’in da ya aikata laifin, zaune suke gida daya da iyayen yarinyar da ya yi wa fyaden.
Ya zuwa rubuta wannan labara, rundunar ta ce tana nan tana gudanar da binciken dalilan da suka sanya ma’aikacin nata ya tafka wannan abun tsiya. Da zarar an kammala bincike za su mik ashi ga shugabansu don daukar mataki na gaba.