An kama dan sanda da satar jarabawar JAMB
Hukumar shirya jarabawar shiga manayan makarantu (JAMB) ta damke wani jami’in dan sanda bayan ya dauki hayar wani ya rubuta masa jarabawa. Dan sandan ya yi rajistar jarabawar JAMB ta UTME ne da sunansa amma ya bayar da hoto da sauran bayanan sojan hayan da zai rubuta amsa jarabawar. “Na je JAMB ne su sauya […]
Hukumar shirya jarabawar shiga manayan makarantu (JAMB) ta damke wani jami’in dan sanda bayan ya dauki hayar wani ya rubuta masa jarabawa.
Dan sandan ya yi rajistar jarabawar JAMB ta UTME ne da sunansa amma ya bayar da hoto da sauran bayanan sojan hayan da zai rubuta amsa jarabawar.
“Na je JAMB ne su sauya min hotona (a Akwa Ibom) amma suka ce min ba zan iya amfani da sakamakon jarabawar ba saboda hoton”, inji shi.
Da yake wa ’yan jarida bayani, dan sandan da ke aiki a Jihar Akwa Ibom ya ce ya biya sojan hayan N30,000 ya rubuta masa jarabawar, saboda a lokacin an tura shi wani aiki na musamman.
- Za a bude makarantun Gwamnatin Tarayya 12 ga Oktoba
- Gwamnan Bayelsa: Kotu ta tabbatar da nasarar Douye Diri
- An kama mafarauta suna fashi a Adamawa
Ya ce bayan ya samu maki 240 a jarabawar ne ya fara kokarin samun gurbin shiga jami’a amma aka ce masa hakan ba zai samu ba saboda bambancin hotunan.
Dalilin haka ne ya je ofishin JAMB yana neman a sauya masa hotonsa inda a nan aka cika hannu da shi.
Kawo yanzu dai jami’in yana rokon hukumar da ta sassauta masa yana mai alkawarin taimaka mata wajen binciken masu yin sojan gona a jarabawar.
Sai dai Shugaban hukumar, Farfesa, Ishaq Oloyede, ya ce za a gurfanar da jami’in kamar yadda doka ta tanadar.
Ya ce dan sandan na daga cikin dalibai 657 da suka bukaci hukumar ta sauya musu hotunansu, amma da aka titsiye shi sai ya kasa bayar da gamsasshen bayani kafin daga baya ya shaida wa hukumar cewa wani ne ya rubuta masa jarabawar.
Farfesa Oloyede ya bayyana damuwa bisa yadda wasu masu neman gurbin karatu ke bullo da sabbin dabaru, duk kuwa da tsauraran matakan dakile magudin jarabawar da hukumar ta sanya.