An kama dan sanda kan yi wa ’yar shekara 13 fyade

Wadanda ake zargin sun rika yaudarar yarinyar suna lalata da ida ne bayan sun sayi kaji a wurinta.

An kama dan sanda kan yi wa ’yar shekara 13 fyade

Fydae

An kama wani jami’in dan sanda bisa zargin sa yi wata yarinya ’yar shekara 13 fyade a Jihar Neja.

Kwamishinar Harkokin Mata ta Jihar, Hajiya Hadiza Kuta, ta sanar da cewa dan sanda da wasu mutum biyu da ake zargi sun sha yi wa wa yarinyar fyade.

Ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) cewa wadanda ake zargin sun rika yaudarar yarinyar suna lalata da ida ne bayan sun sayi kaji a wurinta.

Hajiya Hadiza ta kuma bayyana damuwa kan yadda daga baya aka yi kokarin kawar da maganar zargin fyaden, ta hanyar zargin yarinyar da sata.

A cewarta, bayan iyayen yarinyar sun ga cewa duk kokarinsu na sama wa ’yar tasu adalci ya gagara, sai suka kawo wara ma’aikatar kara domin samun taimako.

“Iyayen yarinyar sun shaida wa ma’aikatar cewa kokarinsu na samun adalci ya yi ta samun turjiya, don haka suka yanke shawarar kawo kara domin samun dauki,” a cewar ta tana mai bayyana illar dora wa ’ya’ya talla.

Kwamishinar ta ba wa iyayen yarinyar tabbacin samun adalci, a yayin da take nuna damuwa kan yawaitar matsalar yi wa kananan yara fyade a jihar

Ta yi alkawarin tabbatar da ba wa yarinyar cikakkiyar kulawa da kariya, musamman la’akari da yadda fyade ke illa ga rayuwar wadanda aka yi musu cin zarafi ta hanyar jinsi.

Ta bayyana takaici bisa yadda ake yawan saurin bayar da belin wadanda ake zargi da aikatawa, jim kadan bayan an gurfanar da su a gaban kotu.

A karshe ta bayar tabbacin ganin an gudanar a bincike mai zurfi tare da hukunci ga duk wanda ke da hannu a cin zarafin yarinyar. (NAN)