An kama dan sanda mai kula da ma’ajiyar makamai da kokarin sace bindigogi
Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta gabatar da wani jami’inta da ke kula da ma’ajiyar makamanta da wasu mutum biyu da take zargin ta kama su a lokacin da suka fasa ma’ajiyar makamanta suka saci bindigogi. Jaridar Premium Times ta ce Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Umar Ambursa ne ya bayyana haka lokacin gabatar da wadanda […]
Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta gabatar da wani jami’inta da ke kula da ma’ajiyar makamanta da wasu mutum biyu da take zargin ta kama su a lokacin da suka fasa ma’ajiyar makamanta suka saci bindigogi.
Jaridar Premium Times ta ce Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Umar Ambursa ne ya bayyana haka lokacin gabatar da wadanda ake zargin a hedkwatar ’yan sandan da ke Kaduna, inda ya ce, da misalin karfe 11:30 na dare a ranar 20 ga Oktoba, jami’in kula da makaman rundunar Nanbol Audu wanda Na’ibin Sufurtandan ’Yan sanda ne (DSP) ya je ma’ajiyar makaman da wasu mutum biyu da ba sanannu ba ne a wata mota shigar domin su sace bindigogi da harsasai.
Ya ce, an ajiye motar ce a bayan ginin ma’ajiyar makaman inda dan sandan da mutum biyun suka rika dauko makaman suna sanyawa a cikinta.
Kwamishinan ya ce, dan sandan da ke aikin tsaro a lokacin ne ya sha jinin jikinsa ya hana motar fita daga harabar hedkwatar ’yan sandan.
“Lokacin da yake yi musu tambayoyi, sai jami’in kula da makaman ya kasa bayar da gamasasshen bayani kana bin da ya kawo shi, inda hakan ya jawo aka kama shi tare da abokan tafiyarsa a cikin motar da suka hada da wani mai suna Zingkur Joseph da ke zaune a Trade Centre, Jos da Samuel Adamu da ke Kuru a karamar Hukumar Jos ta Kudu dukkansu daga Jihar Filato,” inji Kwamishinan.
Ya kara da cewa: “A lokacin binciken an same su da bindigogi kirar G3 guda 11 da aka boye a kasar kujerun motar.”
KwamishinaAmbursa ya kara da cewa bincike ya nuna daya daga cikin fararen hular biyu makeri ne da ya kware wajen kera bindigogi.
“Wadanda ake zargin biyu sun zo ne daga Jos a Jihar Filato domin sayen bindigogin daga jami’in kula da makaman kan Naira dubu 400,” inji Kwamishinan.
Sauran shaidun da aka samu daga wadanda ake zargin sun hada da tsabar kudi Naira dubu 400 da mota marsandi kirar 230-E mai launin ruwan dorawa, mai lambar Jihar Filato LGT 588, RJ da aka yi amfani da ita don boye bindigogin.