An kama dan sanda ya sato karafunan titin jirgin kasa

An kama shi motarsa makare da karafunan titin jirgin kasa da ya sato.

An kama dan sanda ya sato karafunan titin jirgin kasa

Dubun wani tsohon hafsan dan sanda ta cika bayan jami’an tsaron kaya (DSS) sun kama shi dumu-dumu ya sato karafan titin jirgin kasa.

Jami’an na DSS sun cafke tsohon sufetan dan sandan ne a cikin dare ranar Talata, motarsa makare da karafunan titin jirgin kasan a garin Jos, Jihar Filato.

“An kama wani tsohon dan sanda mai mukamin Sufeta, Garba Audu, tare da wasu mutum biyar. Shi ma manajan tashar jirgin kasa da ke Bukuru yana nan an tsare shi.”

Darakan Ayyuka na DSS a Jihar Filato ya ce bayan an matas wa tsohon dan sandan da aka kama ne da tambayoyi ya fallasa sauran mutum biyar din da suka sato wayoyin lantarki tare.

Ya ce tsohon Sufetan dan sandan ya kai su wani suto da suke adana kayan satan inda aka gano wayoyin lantarki, baya ga karafunan titin jirgin kasa cikin mota shida.

Ya ce kara da cewa kayan satan sun kuma hada da manyan kulli 18 na mayan wayoyin lantarki.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna