An kama dan shekara 23 da kunshi 605 na tabar wiwi a Kano

Matashin da aka kama da sinki 605 na tabar wiwi ya ce shi bai taba dandawa ba

An kama dan shekara 23 da kunshi 605 na tabar wiwi a Kano

Wani tulin kayan tabar wiwi da Kwastam ta kwace a Legas ranar 2 ga Afrilu, 2021

Wani wani matashi mai shekara 23 da aka kama shi da kunshi 605 na tabar wiwi a unguwar Kofar Mata da ke Karamar Hukumar Birni ta Jihar Kano, ya shaida wa jami’an tsaro cewa a rayuwarsa bai taba sanin ta ba, ballantana ya taba sha.

’Yan sanda sun ce sun cafke matashin ne da buhuna makare da tabar wiwi, bayan mazauna unguwar Kofar Mata sun kai korafi cewa dilolin miyagun kwaya sun addabi unguwar.

“Bayan samun korafi daga mazauna unguwannin Kofar Mata da Mandawri game da wani dilan miyagun kwayoi da ke sayar wa matasan unguwannin, Kwamishinan Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Muhammed Usaini Gumel ya ba da umarni aka kamo wanda ake zargin a unguwar Kofar Mata.

“Amma wanda ake zargin dan asalin unguwar Rijiyar Lemo da ke Karamar Hukumar Dala ne, kuma shekarunsa 23

“A yayin bincike an gano kunshi 605 na ganyen da ake zaton tabar wiwi ce ” in ji sanarwar da rundunar ta fitar.

Da yake gabatar da wanda ake zargin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Muhammed Usaini Gumel ya ce matashin ya yi ikirarin cewa shi sana’ar gwangwan yake yi a Legas, da zai zo Kano ne wani abokinsa ya ba shi sakon ya kawo masa gida.

Matashin ya ce, Na zo gida ne daurin aure daga Legas; Da zan zo ne wani abokina ya ba ni sakon wadannan buhunan in kawo masa gida.”

A cewarsa, “Ni ban san cewa wiwi ba ce a ciki, saboda a rayuwa ta ban taba sha ba — ko sanin ta ban yi ba.”

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Kano: Kwamishinan da Abba ya tsige ya koma Jam’iyyarAPC