An kama dan shekara 35 da yi wa ‘yar shekara uku fyade
Dubun wani mutum dan shekara 35 da ya yi wa ‘yar shekara uku fyade ya cika, bayan da ya shiga komar ‘yan sanda, inda ya amsa laifinsa ya kuma danganta lamarin da aikin shaidan. Mahaifiyar yarinyar wace ke haya a gida daya da wanda ake zargin a yankin Sango Ota a Jihar Ogun, ita ta […]
Dubun wani mutum dan shekara 35 da ya yi wa ‘yar shekara uku fyade ya cika, bayan da ya shiga komar ‘yan sanda, inda ya amsa laifinsa ya kuma danganta lamarin da aikin shaidan.
Mahaifiyar yarinyar wace ke haya a gida daya da wanda ake zargin a yankin Sango Ota a Jihar Ogun, ita ta kai kara ga ‘yan sanda bayan da ta ga alamar jini a jikin wandon yarinyar, bayan da ta kula da kyau sai ta ga jinin na fitowa ne daga gaban yarinyar, lamarin da yasa ta tambaye ta sai ta ce mutumin mai suna Ayegunle Adekunle ne ya kai ta dakinsa ya yi amfani da ita, hakan yasa mahaifaiyar yarinyar ta shigar da kara ofishin ‘yan sanda.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda ya alakanta laifin da aikin shaidan, “tuni kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ahmad Iliyasu ya bada umarnin tisa keyar wanda ake zargin zuwa sashin binciken miyagun laifuka na rundunar.
Ko a baya bayan nan ‘yan sandan sun samu nasarar kame wani mutum mai suna Abiodun Ojo mai shekara 38 da ake zargi da yi wa yarinya ‘yar shekara shida fyade bayan da ya yaudare ta ya kai ta wani daji da ke daura da gidan da yake haya tare da iyayenta, a kusa da kan iyakar kasa ta Idiroko, kururuwar da yarinyar ta yi ne ya sa mutanen yankin suka farga, inda suka lakada masa dan karen duka kafin daga bisani su damka shi ga ‘yan sanda, inda jami’an suka gaggauta kai yarinyar zuwa asibiti domin ceto rayuwarta kamar yadda mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi ya shaida wa Aminiya a wannan makon.