An kama dattijo mai yaɗa hotunan tsofaffin ’yan matansa a Bauchi
Ya yaɗa hotunan matan da ya nema tsawon shekaru shida zuwa 20 a Bauchi.
Hukumar Hisba a Jihar Bauchi, ta kama wani mutum mai kimanin shekaru 76 mai suna Bala Muhammad bisa zargin yaɗa hotunansa tare da tsofaffin ’yan matan da ya nema a dandalin sada zumunta.
Wannan aiki da Bala ya yi ya janyo mutuwan aurarraki da dama sannan ya harzuka ’yan uwa da mazaje da iyalan waɗanda ya wallafa hotunan da suka ɗauka tare a dandalin sada zumunta.
Shi dai Bala ya bayyana a cikin hotuna kusan 30 tare da mata daban-daban masu matsakaicin shekaru.
Hotunan sun janyo cece-ku-ce a shafukan sada zumunta, inda da yawa suka buƙaci magidanta a Bauchi da su yi wa matansu shamaki da Bala Muhammad.
Da yake zantawa da manema labarai, kwamishina da ke kula da sashen Hisbah na Jihar Bauchi, Barista Aminu Balarabe Isah, ya ce hukumar ta samu korafe-korafe da dama daga iyalan matan da ya wallafa hotunansu kuma an yi kokarin kama shi a gidansa amma ba a yi nasara ba.
Sai dai ya ce jami’an ’yan sanda sun kama shi kuma sun miƙa Hukumar Hisbah shi domin gudanar da nata binciken kafin daga bisani ta mayar da shi hannun ’yan sandan.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai, mutumin da ake zargi ya tabbatar da hotunan da ke yaduwa, inda ya ce an ɗauki hotunan ne kimanin shekaru shida zuwa shekaru 20 da suka gabata a lokacin da yawancin matan ba su yi aure ba.
Sai da Bala ya ce yana neman gafarar matan da iyalansu.
Bala mai shekaru sama da 76 wanda ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Dass ta Jihar Bauchi ce ya ce bai taɓa yin aure ba kuma ba shi da ‘ya’ya.
Ya bayyana cewa shi tsohon ma’aikaci ne da ya yi aiki har ya kai muƙamin Darekta da ke kula da harkokin mulki kuma ya yi ritaya daga aikin gwamnati a shekarar 2016.
Bala ya ce shi dai musulmi ne amma ba ya gudanar da addinin musulunci kamar yadda yake a shari’ance, illa iyaka duk abin da zai yi yakan aiwatar ne bisa sha’awa da nishaɗi.
Sai dai ya ce tun kafin shigarsa hannu wani ɗan uwansa ya ja kunnensa kan hotunan da yake yaɗawa amma a yanzu ya yi nadamar aikinsa kuma yana neman afuwa.
Bala ya ce bai taɓa yin aure ba ne saboda duk matar da ya nema sai a kada shi, kuma yanzu zai yi aure idan ya samu amma matar ta kasance ta yi karatu kuma tana da ɗan aikin da ta ke yi.