An kama dilan kwaya zai kai sansanin Boko Haram
NDLEA ta cafke mai juna biyu da wasu mata hudu da ke fataucin miyagun kwayoyi
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta kama wani dillalin miyagun kwayoyi a hanyarsa ta kaiwa sansanin mayakan Boko Haram kwayoyin a yankin Banki da ke Jihar Borno.
Mutumin mai shekaru 42 na daga cikin manyan dilolin miyagun kwayoyi 24 da hukumar ta kama a sassan Najeriya, cikinsu har da wata mai juna biyu da wasu mata hudu.
Kakakin hukumar NDLEA na kasa, Femi Babafemi, ya ce an kama miyagun kwayoyi na musamman da nauyinsu ya kai kilogram 7,609 a hannun dilolin kwayar a jihohi takwas.
Ya ce: “Yawancin kamen an yi ne a Jihar Nasarawa inda aka kama wata babbar mota dauke da manyan jakunkuna makare da tabar wiwi da ta kawo daga Aure, Jihar Ondo, kuma an kama mutum uku masu alaka da kayan.
“A Abuja ma an kama wasu mutum biyu da sinki 80 na curarren tabar wiwi da kuma jakunkuna 169 na tabar wiwi mai nauyin 1,961.5kg a cikin wata babbar mota.
“Sai Borno inda aka kama wani dan shekara 42, da ke kai wa ‘yan ta’adda kwayar a yankin Banki, da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru.
“Akwai kuma wata mai juna biyu, wata kuma a cikin dilolin kwaya guda shida da suka shiga hannu a Jihar Anambra,” in ji Femi Babafemi.