An kama dilar kwayoyi da kilogiram 5,862 da yaranta 6 a Legas
Sai dai an yi ba-ta-kashi kafin a samu nasarar kama su.
Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) sun kama wata hamshakiyar dilar kwayoyi a Jihar Legas da kilogiram 5,862 na miyagun kwayoyin.
A ranar Asabar ne dai aka kama Sherifat Kehinde Lawal, wace ta kware wajen safara da sayar da miyagun kwayoyi a cikin jihar tare da wasu mutum shida masu tallafa mata.
- Dakarun Rasha na daf da mamaye babban birnin Ukraine
- Dokar hana kiwo: Za a ci tarar N100,000 kan kowace saniya a Delta
A wata sanarwar da mai magana da yawun hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar ya ce hukumar ta yi nasarar babban kamun ne sakamakon bayanan sirrin da ta samu na hada-hadar miyagun kwayoyi a unguwannin Osho da Gambari da Beecroft duk a cikin garin na Legas.
Kakakin ya ce jami’an nasu sun yi wa yankunan kawanya da safiyar Asabar, inda suka samu nasarar kamar mutanen.
“Bayan da jami’anmu suka kamo wadanda ake zargin ne, sai ragowar gungun masu safarar miyagun kwayoyin suka yin kan jami’anmu da jifa da kwalabe har da harbi da bindiga, domin hana mu cigaba da kamen tare da kokarin kubutar da wadanda muka kama,” inji kakakin na NDLEA.
Sai dai ya ce jami’an sun yi kokarin kare kansu, sannan sun tafi da wadanda ake zargin su bakwai.
Sauran mutum shidan da aka kama tare da Sherifat sun hada da Ahmed Yisau da Solomon Alape sai Olayemi Akinola da Salami Qudus da Bakare Rafiu sai Rose Samson da Yusuf Rofiat da kuma Chukwudi Egon.
Femi Babafemi ya kuma ce Shugaban hukumar ta NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya) ya yaba wa jami’an rundunar da ke aiki a Jihar ta Legas bisa nasarar da suka yi a aikin.
Buba Marwa ya kuma gargadi zauna gari banza da masu safarar miyagun kwayoyi ke amfani da su wajan kai wa jami’an NDLEA hari, da su kuka da kansu.