An kama dillalan kwaya 1,300 a Katsina —NDLEA

Hukumar NDLEA ta kwace ton 1.3 na miyagun kwayoyi daga hannun wadanda aka kama.

An kama dillalan kwaya 1,300 a Katsina —NDLEA

Dillalan kwaya akalla 1,344 a Jihar Katsina ne suka shiga hannun Hukumar Hana Shafa da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) a cikin shekara guda.

Hukumar NDLEA reshen Jihar Katsina ta ce an kama dillalan kwaya da masu safaran nata ne a shekara guda da ta gabata.

Kakakin hukumar a jihar, Hassan Abubakar, ya sanar ranar Alhamis cewa hukumar ta kwace ton 1.3 na miyagun kwayoyi daga hannun wadanda aka kama.

Ya bayyana cewa kwayoyin sun hada da tabar wuri da wasu kwayoyi masu hadari.

Ya sanar da haka ne a yayin shirye-shiryen Ranar Yaki da Miyagun Kwayoyi ta Duniya ta 2024.

Abubakar ya ci gaba da cewa hukumar ta wayar da kan sama da mutane 56,000 kan illolin tu’ammali da miyagun kwayoyi, ta ba wa 136 shawarwari tare da daure wasu 107, wasu shari’o’i 120 kuma na gaban kotu.