An kama dillalin da ke samar da makamai ga Boko Haram

Hukumomin sojin Najeriya sun bayyana cewa sojojin hadin-gwiwa ta gabar Tafkin Chadi sun kama wani babban dillalin makamai da ke samar da makamai ga kungiyar Boko Haram.Wata majiyar tsaro ta tabbatar wa gidan rediyon BBC cewa, sojojin Najeriya da hadin gwiwar takwarorinsu na Chadi sun kama mutumin mai suna Babagana Gwange a cikin kasar Chadi […]

An kama dillalin da ke samar da makamai ga Boko Haram
An kama dillalin da ke samar da makamai ga Boko Haram

Hukumomin sojin Najeriya sun bayyana cewa sojojin hadin-gwiwa ta gabar Tafkin Chadi sun kama wani babban dillalin makamai da ke samar da makamai ga kungiyar Boko Haram.
Wata majiyar tsaro ta tabbatar wa gidan rediyon BBC cewa, sojojin Najeriya da hadin gwiwar takwarorinsu na Chadi sun kama mutumin mai suna Babagana Gwange a cikin kasar Chadi a ranar Talatar da ta gabata.
Bayanai na nuna cewa Babagana Gwange shi ne babban mai yi wa kungiyar Boko Haram safarar makamai.
An dade ana kokarin gano inda ’yan Boko Haram ke samun manyan makamai da suke kai hare-hare a kan fararen hula a Najeriya da makwabtanta.
kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ke gabar Tafkin Chadi da kuma Jamhuriyyar Benin sun kafa rundunar kawance ta sojoji domin kawo karshen ayyukan Boko Haram da suka jefa miliyoyin mutane cikin mawuyacin hali.
Kuma a karshen wannan wata ne rundunar za ta soma aiki domin fatattakar ’yan Boko Haram.
Wannan nasara ta kama babban dillalin makaman na Boko Haram ta zo ne a daidai lokacin da maykan Boko Haram din suka fusata tare da kaddamar da hari a garin Buratai, mahaifar Babban Hafsan Sojin kasa na Najeriya Manjo Janar Tukur Yusuf Burutai, inda suka kone gidaje ciki har da na ’yan uwansa. Janar Burutai ya sha alwashin murkushe mayakan Boko Haram da ke addabar Arewa.
Akalla mutum biyu sun mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata a harin na Burutai, kamar yadda wasu mazauna garin suka tabbatar wa Kamfanin Dillacin Labarai na Reuters.
Majiyoyi sun ce an kai harin ne a ranar Talata, sai dai lokacin da aka kai harin Janar Burutai ba ya cikin garin.
Janar Tukur Buratai dai shi ne sabon babban hafsan sojin Najeriya da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada, wanda ya sha alwashin murkushe ayyukan mayakan Boko Haram.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos