An kama dillalin makamai a hanyar Kaduna zuwa Abuja
Rundunar sojojin Najeriya ta yi nasarar kama wani kasurgumin dillalin muggan makamai da yake kaiwa ‘yan bindigar da suka addabi hanyar Kaduna zuwa Abuja wanda suke takura matafiya a hanyar. Rundunar sojojin da ke da cibiya a Kaduna sun yi nasarar kama dillalin mai suna Alhaji Shehu, wanda gidansa ya ke unguwar Sabogaya, cikin Karamar […]
Rundunar sojojin Najeriya ta yi nasarar kama wani kasurgumin dillalin muggan makamai da yake kaiwa ‘yan bindigar da suka addabi hanyar Kaduna zuwa Abuja wanda suke takura matafiya a hanyar.
Rundunar sojojin da ke da cibiya a Kaduna sun yi nasarar kama dillalin mai suna Alhaji Shehu, wanda gidansa ya ke unguwar Sabogaya, cikin Karamar Hukumar Chikun a jihar Kaduna.
An kuma yi nasarar kama wasu mutum biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, suna kokarin karbar hayar bindigogin AK47 don gudanar hare-hare.
Mataimakin Diraktan sashin hulda da jama’a na rundunar ta1 Division, Kanal Ezindu Idimah ya tabbatar da kamen cikin wata sanarwa da ya fitar a Kaduna. Ya ce, an kama dillalin bindigogin a ranar Asabar dauke da bindigogin kirar AK47 guda 6.