An kama dillaliyar jariri a Akwa Ibom
Dubun wata mata mai suna Imaobong Udoh ya cika a yunkurin dillancin sayar da jariri da ta yi kan Naira 260,000 ga wasu attajirai kuma yanzu haka ita da dillalanta da suka kulla cinikin, Regina James da mijinta Mfon James duk sun shiga hannu.Aminiya ta samu tabbacin matar da ta haifi jaririn mai suna Comfort […]

Dubun wata mata mai suna Imaobong Udoh ya cika a yunkurin dillancin sayar da jariri da ta yi kan Naira 260,000 ga wasu attajirai kuma yanzu haka ita da dillalanta da suka kulla cinikin, Regina James da mijinta Mfon James duk sun shiga hannu.
Aminiya ta samu tabbacin matar da ta haifi jaririn mai suna Comfort Henry da likitan da ta haihu a asibitinsa mai suna Emmanuel Okon da ya kulla cinikin su ma duk suna hannun ’yan sanda. Ana jin cewa attajirin da zai sayi jaririn ya bayar da awalajar Naira 150,000 daga bisani, bayan an kawo masa jaririn, ya cika Naira 110,000.
Tun farko a jawabin da kwamishinan ’yan sandan Jihar Akwa Ibom ya yi wa manema labarai game da badakalar, ya ce shi Okon ne ya shirya cinikin kuma ya yi alkawarin kawo masu sayen jaririn kauyen Nna-Enin da ke karamar Hukumar Uruan.
Sai dai Mista Mfon James ya shaida wa ’yan jarida cewa matarsa ba ta gaya masa gaskiya cewa sayen jaririn ta yi ba, domin, a cewarsa, “Matata Regina ta taba shaida min cewa tana da juna biyu kuma ta haifi ’ya’ya hudu, uku sun mutu saura daya. Tunda ni ba mazaunin gida ba ne ba ni da masaniya, ashe yaro sayensa aka yi”. Inji shi.