An kama direban da ya yi wa fasinjarsa fyade
Daga hawa motarsa ya yi cikin jeji da ita ya yi mata fyade ya kwace kudadenta
Dubun wani dirabe ta cika bayan ya yi garkuwa da wata fasinjar da ta hau motarsa ya kuma yi mata fyade.
Matar ta hau motar hayar ce a hanyar Ogunrun zuwa wurin aikinta, a Legas amma direban ya tsere da ita ya kai ta cikin jeji, ya yi mata dukan kawo wuka da kuma fyade.
- ‘Yadda muke shiga kunci yayin zaman zawarci’
- An kama limamin da ya daura wa gawa aure a Bauchi
- Gobara ta tashi a masana’antar rigakafin COVID-19
Ta ce bayan ya yi mata fyade, sai ya tsare ta a cikin jejin ya sa ta kira danginta suka tura mata N140,000.
Bayan dan uwanta ya tura mata kudin sai direban ya sa ta tura masa su zuwa wani asusun banki sannan ya sake ta.
Kakakin ’yan sandan Jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi, ya ce matar ta bayyana cewa daidai mahadar Mowe Junction ne direban ya sauya hanya ya doshi Ibadan a guje, inda a hanya ya yi mummunan aikin.
Oyeyemi ya ce bayan matar ta kai kara ne DPO na Mowe, Marvis Jayeola, ya sa aka shiga binciken ganowa da kuma kama wanda ake zargin.
Ya ce a watan Satumban 2020 ne mutum da aka kama a ranar 16 ga watan Janairun 2021 ya yi wa fasinjar fashin.
Kakakin ’yan sandan ya ce direban ya amsa cewa ya aikata laifin, kuma Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Edward A. Ajogun, ya sa Sashen Yaki da Ayyukan Garkuwa da Mutane da Sauran Manyan Laifuka su zurfafa bincike kafin a gurfanar da shi a kotu.