An kama Dodanni kan zargin fashi da makami a Ondo
’Yan sanda sun kama wasu Dodanni guda biyu da ake zargi da hannu wajen aikata fashi da makami ga wani mazaunin yankin Melege da ke Karamar Hukumar Owo ta Jihar Ondo. Dodannin, wadanda aka bayyana sunayensu a matsayin Sheriff Ojo da kuma Muhammed Lukman, sun shiga hannu ne kan zargin yin fashin kudi N370,000 da […]
’Yan sanda sun kama wasu Dodanni guda biyu da ake zargi da hannu wajen aikata fashi da makami ga wani mazaunin yankin Melege da ke Karamar Hukumar Owo ta Jihar Ondo.
Dodannin, wadanda aka bayyana sunayensu a matsayin Sheriff Ojo da kuma Muhammed Lukman, sun shiga hannu ne kan zargin yin fashin kudi N370,000 da wayar salula ga wani mai suna Adinoyi Mohammed.
- Babu ma’aikacin da zai sake shiga ofis muddin bai yi rigakafin COVID-19 ba – Gwamnati
- Najeriya a Yau: Shin Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet Zai Kawo Karshen Magudin Zabe?
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Funmi Odulami ce ta tabbatar da kamen.
A cewarta, “Mun kama wadanda ake zargin ne wadanda suka yi shigar dodanni, sannan suka ji wa Adinoyi Mohammed raunuka da adduna, suka kwace masa kudi N370,000 da wayar salula wacce darajarta ta kai N32,000 da kuma riga wacce ita kuma kimarta ta kai N2,500.
“Kazalika, sun kuma ji wa Mahaifin Adinoyin, mai suna Saliu Ajayi, rauni kafin su bar wurin da suka aikata ta’asar, amma jami’an tsaron da ke garin suka samu nasarar kama su.
“Mun sami nasarar kwace adduna guda biyu daga hannunsu da kayan tsafi da rigunan dodanni, tare da kama dodanni biyu.
“Nan ba da jimawa ba za mu gurfanar da su a gaban kotu, yayin da muke ci gaba da kokarin kamo ragowar wadanda suka gudu,” inji Kakakin.