An kama dodo kan cin zarafin mata
An gurfanar da wani dodo a bisa zargin sa da cin zarafin wata mata a yanin Ugwuoye da ke garin Nsukka a Jihar Enugu. Rundunar ’yan sanda reshen Nsukka ce ta gurfanar da dodon, wanda aka fi sani da Oriokpa a gaban wata kotun majistare a ranar Alhamis. Sanarwa da kakakin rundunar, Daniel Ndukwe, ya […]
An gurfanar da wani dodo a bisa zargin sa da cin zarafin wata mata a yanin Ugwuoye da ke garin Nsukka a Jihar Enugu.
Rundunar ’yan sanda reshen Nsukka ce ta gurfanar da dodon, wanda aka fi sani da Oriokpa a gaban wata kotun majistare a ranar Alhamis.
Sanarwa da kakakin rundunar, Daniel Ndukwe, ya fitar, ta bayyana cewa, binciken da aka gudanar a kan lamarin ya gano wanda ake zargin yana cikin gungun wasu dodannin da suka afka wa wata ma’aikaciyar jinya da ke kan babur a cikin watan Afrilu.
Amma daga baya aka bada belinsa.
Sanarwa tace ana ganin wanna dodon da aka kama kamar shine aka gani a hoton bidiyon da ya karade kafafen sadarwa.
“Yau, 22 ga Mayu, 2024, an gurfana da wani dodo a gaban kotun majistare da ke Nsukka a jihar Enugun Najeriya, amma kotu ta bayar da belin sa.
“A halin da ake ciki, kwamishinan ’yan sanda, Kanayo Uzuegbu, ya yi Allah wadai da wannan aika-aika, sannan ya gargadi masu fakewa da sunan bikin al’ada suna cin zarafin al’umma da su daina.
“Ya jaddada cewa daga yanzu rundunar ba za ta raga wa duk wanda aka kama, kamar yadda yake a halin yanzu,” in ji.