An kama falke da buhun wiwi 104
A wani samamen da suka kai kauyen Ikot-Nkese da ke karamar Hukumar Bakassi a Jihar Kuros Riba ’yan sanda sun yi katarin damke wani dillalin wiwi a mazaunin kauyen Edet Okon, inda aka kama shi da tarin buhun wiwi 104 da jarkoki biyu masu daukar lita 100 da 200 da aka jika wiwi a cikinsu. […]
A wani samamen da suka kai kauyen Ikot-Nkese da ke karamar Hukumar Bakassi a Jihar Kuros Riba ’yan sanda sun yi katarin damke wani dillalin wiwi a mazaunin kauyen Edet Okon, inda aka kama shi da tarin buhun wiwi 104 da jarkoki biyu masu daukar lita 100 da 200 da aka jika wiwi a cikinsu. Sai dai wanda ake zargin ya kekasa kasa ya ce atafau ba ya da masaniya kan wadannan buhuna da jarkokin tabar wiwin.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kuros Riba Hogan Bassey ya shaida wa manema labarai cewa jama’ar gari ne suka kyankyasa wa rundunarsu halin wanda ake zargin inda suka yi masa sammako suka kame shi. “Jami’anmu sun kama shi da buhuna tabar wiwi 104 da wasu jarkokin masu cin lita 100 da 200 da aka jika wiwi a cikinsu, kuma nan take aka tasa keyarsa zuwa hedkwatarmu”inji Bassey.
Hogan Bassey ya c da zarar sun gama bincike za su mika wanda ake zargin ga hukumar yaki da miyagun kwayoyi (NDLEA), ta yi nata binciken ta kuma mika shi ga kotu.
Aminiya ta ji ta bakin Edet Bassey wanda aka kama kan zargin, inda ya ce “Ni ba ni da wata masaniya game da wadannan kaya, ba nawa ba ne ban kuma san mai su ba.” Amma da aka kara tambayarsa idan abin da ya fadi gaskiya ne yaya aka yi aka same su a gidans sai ya kasa yin bayani.