An kama fasto bisa zargin safarar mata zuwa Kuwait

Rundunar ’yan sandan Jihar Oyo ta yi nasarar kubutar da wasu mata biyu daga ayyukan bauta a kasar Kuwait da yanzu haka aka dawo da su gida Najeriya. ’Yan sandan sun kama mutumin da ya yi safarar matan zuwa Kuwait, mai suna Fasto bictor Adelaja na cocin Lebites Christian Centre da ke Ibadan. Faston ya […]

An kama fasto bisa zargin safarar mata zuwa Kuwait
An kama fasto bisa zargin safarar mata zuwa Kuwait

Rundunar ’yan sandan Jihar Oyo ta yi nasarar kubutar da wasu mata biyu daga ayyukan bauta a kasar Kuwait da yanzu haka aka dawo da su gida Najeriya.

’Yan sandan sun kama mutumin da ya yi safarar matan zuwa Kuwait, mai suna Fasto bictor Adelaja na cocin Lebites Christian Centre da ke Ibadan. Faston ya yi amfani da kamfanin safarar mutane na Eleos Golden Herritage Limited ne wajen zolayar wadannan mata ta hanyar yi musu karyar sama musu ayyuka masu gwabi a gidajen sayar da man fetur da gas da aikin banki da nas-nas a asibitoci da koyarwa a makarantu amma a maimakon haka sai wadannan mata masu suna Biola Daramola ’yar shekaru 26 da Christiana Ajayi mai shekaru 29 suka tsinci kansu tare da da wasu matan da suka fito daga wasu kasashen Afirika da ake kulle su cikin daki daya mai bahaya daya tak ana fitowa da su da safe domin tilasta musu yin ayyuka da suka yi kama da bauta.
“Ayyuka masu tsananin gaske muke yi daga safiya zuwa yammacin kowace rana ba hutawa kuma sau daya muke cin ragowar abincin da za a zuba cikin kwandon shara.” Inji Biola Daramola. “Sharar kazantar kowane sashe na cikin wani gida mai hawan bene uku da wanke-wanken kayayyaki da suturu da goge su da wankin dakunan bahaya da sauran ayyukan ukuba da makamantansu ba tare da biyanmu ladan aiki kamar yadda muka yi yarjejeniya tun farko da Fasto Adelaja a Najeriya ba.”
Duk da yake faston bai musanta wannan batu ba sai dai ya yi karin bayani domin kare kansa kamar haka: “Kafin tafiyar wadannan mata zuwa Kuwait, na zauna tare da su na yi musu bayanin cewa, da farko kafin su samu ’yancin kai sai sun yi aikace-aikacen cikin gidaje na tsawon watanni 6, sannan daga baya su fara gudanar da irin ayyukan jin dadin rayuwa. Na yi mamakin bayanan da matan suka yi a game da irin ayyukan da suka fara yi da suka kasa jurewa. Ni dai ba ni da masaniyar irin ayyukan bauta da suke cewa ana sa su yi.”
Da yake nuna wadannan mutane ga taron ’yan jarida a ofishinsa da ke Ibadan, Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Oyo, Alhaji Muhammad Musa Katsina, ya ce: “Fasto bictor Adelaja ya yi aiki a matsayin babban manaja a wani banki da aka kore shi daga aiki a cikin shekara ta 2006 a dalilin zambatar bankin kudade masu yawa, wanda yanzu haka hukumar EFCC take bincike a kai. Bayan lafawar al’amarin ne, ya bude wani coci mai suna Lebites Christian Centre da kamfanin safarar mutane zuwa kasashen waje mai suna Eleos Golden Heritage Ltd, dukkansu a Ibadan ya nemi wadannan mata (ba su kadai ba) suna da yawa dukkansu mabiyan cocinsa ne, ya yi musu karyar samun ayyuka a gidajen sayar da man fetur da gas da asibiti da banki da makarantu a kasashen Kuwait da Saudi Arabiya da wasu kasashen Larabawa, sannan ya yi musu takardun bogi aka tura su zuwa kasar Kuwait. Wani dan kasar Habasha mai suna Ibrahim shi ne ya karbe su a filin jiragen sama na Kuwait wanda ya kwace fasfo dinsu daga hannayensu ya kai su wani gida ya kulle su kamar dabbobi a cikin daki daya tare da wasu mata ’yan kasashen Ghana da Saliyo da Benin, ya gaya musu cewa daga yanzu za su fara yin ayyukan kwantaragi babu zabi na tsawon shekaru biyu kafin su samu ’yancin kansu.”
“Irin ukubar da daya daga cikin matan ta gane wa idanunta a kasar Kuwait ne ya sa ta yi yunkurin kashe kanta ko kuma dawowa gida Najeriya ko ta wane hali. Daga nan Ibadan aka kulla wannan makirci aka kyankyashe kwan a Kuwait.” Inji Kwamishina. Ya ce yanzu haka ’yan sanda sun kammala binciken lafiyar wadannan mata biyun da suka tsallake rijiya da baya, an tabbatar da koshin lafiyarsu, an mika su ga iyayensu ba tare da bata lokaci ba. Shi Fasto Adelaja za a gurfanar da shi gaban kotu da zarar an kammala bincike.