An kama Fasto da ‘ya’yansa suna buga jabun kudi
Jami’an tsaron ciki (SSS) sun kama wani Fasto mai suna Godson O. Akubuiro da wadansu mutane 15 saboda zarginsu da laifin buga takardun nairori na jabu.Darektan jami’an tsaro na SSS da ke jihar Kogi Mike Fubara, wanda shi ne ya nuna wa manema labarai wadanda ake zargin, ya ce shida daga cikin wadanda ake zargin […]

Jami’an tsaron ciki (SSS) sun kama wani Fasto mai suna Godson O. Akubuiro da wadansu mutane 15 saboda zarginsu da laifin buga takardun nairori na jabu.
Darektan jami’an tsaro na SSS da ke jihar Kogi Mike Fubara, wanda shi ne ya nuna wa manema labarai wadanda ake zargin, ya ce shida daga cikin wadanda ake zargin ‘ya’yan Fasto Godson Akubuiro ne.
Shi dai Fasto Akubuiro dan shekara 49, wanda dan asalin jihar Imo ne,shi ne jagoran Cocin Mountain of Breakthrough Delekerance Ministry da ke rukunin gidaje na Koya, Igbo Olomu, Ikorodu, Legas, inda a nan ne aka kama shi tare da wadansu da ake zargin nasu.
Darektan na SSS din ya ce sun fara bincike ne watanni hudu da suka gabata domin gano inda ake buga jabun nairorin da suke ta yawo a hannun al’ummomin jihar Kogi, inda suka samu nasarar kama mutane 16 a karkashin jagorancin Rabaran Godson O. Akubuiro.
Abubuwan da aka samu a wurin wadanda ake zargin sun hada da,injuna da wadansu kayyayaki da ake buga jabun kudi da su da jabun kudi masu dimbin yawa da jabun naira miliyan daya da dubu dari uku.
Haka kuma sun samu injunan daukar hoton takarda da launuka iri-iri na fenti.
Rabaran Akubuiro ya tabbatar wa manema labarai cewa lallai sun aikata wannan laifin, inda ya ce shi mutumin Allah ne, amma Shedan ne ya rinjaye shi.
Ya bayyana cewa tun a shekarar 2012 ya fara wannan munmunan aikin a gidansa tare da iyalinsa.
Ya ce ba ya amfanin da jabun kudin wajen biyan bukatun kansa, amma yana amfanin da su ne kawai wajen taimaka wa marasa galihu da mabukata da ke halartar cocinsa.
Sai ya nemi ya a yi masa rangwami, domin kuwa kamar yadda ya ce, sau da yawa mutanen Allah shedan yana fizgarsu, kamar yadda ya yi wa Sarki Dakid na cikin littafin Bible, amma duk haka Allah Ya yafe masa.
Darektan SSS din sai ya bukaci mutane su kara kula domin kada a ba su jabun kudaden da ke yawo a halin yanzu, kuma su hanzarta kai rahoton duk wanda ya ba su irin wannan jabun kudin ga jami’an tsaro.