An kama fasto kan kashe ’yar shekara 13 da duka

Faston ya ce ya firgita ne bayan ya lura yarinyar ta fara raunana, inda nan take ya garzaya da ita zuwa wani asibiti, amma aka tabbatar da rasuwarta.

An kama fasto kan kashe ’yar shekara 13 da duka

’Yan sanda sun kama wani fasto mai shekara 45, Roman Samson, bisa zargin sa da yi wa wata yarinya mai shekara 13, Nancy Peter, bulala har ta mutu, bayan an zarge ta da satar kuɗin mahaifiyarta.

Lamarin ya faru ne a yankin Obanleku da ke Karamar Hukumar Boki ta Jihar Kuros Riba, inda ya jawo ce-ce-ku-ce da fushin mazauna yankin.

Mahaifiyar marigayiyar, Agnes Peter, ta bayyana cewa ta kai ’yarta gidan faston ne a ranar 1 ga watan Yuni domin yi mata nasiha, bayan ta gano cewa Naira 30,000 da ta ajiye a gida sun ɓace.

Agnes ta ce yarinyar ta amsa cewa ita ce ta ɗauki kuɗin, sannan ta bayyana inda ta ɓoye su. Ta ce daga nan ta bar gidan faston domin tabbatar da maganar, inda ta gano kuɗin a cikin wani wandon marigayiyar.

Sai dai, yayin da take dawowa gidan faston, ta ci karo da shi yana gaggawar kai yarinyar asibiti.

Ta ce, “Na haɗu da su a hanya. Ban san cewa ya yi mata duka ba.”

Daga bisani likitoci sun tabbatar da mutuwar Nancy a asibitin.

Rahotanni sun ce faston ya amsa cewa ya yi wa yarinyar bulala tsakanin 13 zuwa 15 ne bayan mahaifiyarta ta koka kan cewa yarinyar ta saba yin sata, amma ya musanta cewa yana da niyyar kashe ta.

Faston ya ce ya firgita ne bayan ya lura yarinyar ta fara raunana, inda nan take ya garzaya da ita zuwa wani asibiti, amma aka tabbatar da rasuwarta.

Rundunar ’yan sandan jihar ta tabbatar da kama wanda ake zargin, tare da bayyana cewa ta fara gudanar da bincike kan lamarin.

Wannan al’amari ya sake tayar da hankula kan yin hukuncin da bulala da kuma yadda ake mu’amala da yara da ake zargi da aikata ba daidai ba.

Mazauna yankin sun bayyana marigayiyar a matsayin yarinya mai fara’a, inda suka ce rasuwarta ta jefa al’ummar yankin cikin jimami.

A halin yanzu, faston na tsare a hannun ’yan sanda, yayin da ake jiran kammala bincike da kuma yiwuwar gurfanar da shi a gaban kotu.