An kama fasto kan lalata da ’yan mata 3 a cocinsa
An kama wani fasto kan zargin lalata da ’yan mata uku a cocinsa da ke Agah a Karamar Hukumar Ilorin ta Kudu a Jihar Kwara. Hukumar tsaro ta Sibil Defens (NSCDC) reshen jihar Kwara ce ta kama faston mai shekaru 45 kan zargin sa da lalata kananan yaran. An ce yaran da faston ya ci […]
An kama wani fasto kan zargin lalata da ’yan mata uku a cocinsa da ke Agah a Karamar Hukumar Ilorin ta Kudu a Jihar Kwara.
Hukumar tsaro ta Sibil Defens (NSCDC) reshen jihar Kwara ce ta kama faston mai shekaru 45 kan zargin sa da lalata kananan yaran.
An ce yaran da faston ya ci wa zarafi ’yan tsakanin shekaru 13 zuwa 17 ne.
Mai magana da yawun hukumar NSCDC a jihar, Ayoola Michael, ya ce wanda ake zargin ya ya kaurin suna wurin cin zarafi da lalata da kananan yara.
Ya ce, hukumar ta kamashi ne bayan korafe-korafe da aka yi ta kawowa kan munanan ayyukansa.
- Rashin tsaro: Za a sauya wa makarantu 359 wurin zama a Kaduna
- ’Yan bindiga sun sace dalibai a Jami’ar Jihar Kogi
Ayoola Michael ya ce, “Bincike ya nuna cewa wanda ake zargin babban malamim Divine Land of Joy Prayer Ministry ne da ke Agah, kuma ya yi lalata da wasu ’yan cocin, kamar yadda wadanda abin ya shafa suka shaida mana.
“Daya daga cikin ’yan matan, wacce ta gwada jarumtaka ta kawo kara, ta bayyana mana munanan abubuwan da suka faru.
“Ta ce, wanda ake zargin ya yaudare ta ne zuwa wani gidan da ba ta sani ba a Sango inda ya yi lalata da ita.
“Ta ce, ya tilasta mata ta rantsewa da baibul kuma ya umurce ta da kada ta fada wa kowa abin da ya faru.
“Sannan ya yi mata barazanar cewa zai iya kashe ta idan ta kuskura ta yi magana da wani kan faruwar lamarin.”
Yarinya ta biyu da faston ya lalata ta ce, faston ya fara lalata da ita ne tun tana ’yar shekara 16.
“Ta ce wanda ake zargin ya yi mata ciki kuma ya ba ta magungunan zubar da cikin, wanda hakan ya haifar mata da zubar jini mai tsanani na tsawon watanni.
“Ita ma wanda ake zargin ya yi barazanar kashe ta idan ta bayyana haramtacciyar alakarsu ga wani mahaluki.”
Ayoola ya ce, “Wadda faston ya yi lalata da ita ta uku ta ce ya fara lalata da ita tun tana da shekara 13 amma ta kasa fada wa kowa, saboda barazanar da ya yi ta cewa za ta mutu idan har ta fallasa shi.”
Ya ce, wanda ake zargin ya amsa laifinsa, ya alakanta wannan mummunar aikin da sharrin shaidan.
Kwamandan NSCDC a jihar Kwara, Dokta Umar J.G Mohammed, ya bayyana damuwarsa kan wannan mummunan aiki, kuma ya ba da umarnin a gudanar da cikakken bincike kan lamarin.