An kama Fasto kan zargin yin lalata da ’yar shekara 16 a Nasarawa
Rundunar ta ce za ta gurfanar da shi a kotu da zarar ta kammala bincike.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa, ta kama wani fasto mai shekaru 37 mai suna Asonye Isaiah, bisa zargin lalata da wata yarinya ’yar shekaru 16 a yankin Karshi.
An kama faston cocin Rock of Love and Adoration Ground da ke yankin tsohuwar Karshi a Abuja.
- An ceto dukkanin fasinjojin da aka sace a Binuwai — Gwamna
- Ana ƙoƙarin shirya min sabuwar maƙarƙashiya — El-Rufai
Jami’an ’yan sanda na ofishin Karshi ne, suka kama shi, kamar yadda Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Nasarawa ta bayyana a ranar Lahadi.
Kakakin rundunar, SP Ramhan Nansel, ya ce an kama faston ne bayan an shigar da ƙorafi a ofishin ’yan sanda ranar 18 ga watan Afrilu, 2026 da misalin ƙarfe 8 na dare.
’Yan sanda sun ce bincike ya nuna cewa wanda ake zargin ya yaudari goggon wadda abin ya shafa da cewa yarinyar tana ɗauke da aljanu kuma tana buƙatar a kai ta wani kogi domin yi mata wankan tsarki.
Sai dai maimakon haka, ana zargin ya kai ta wani otal a Karshi, inda ya yi lalata da ita sau biyu.
Haka kuma, an ce ya yi barazanar kashe ta idan ta faɗa wa wani abin da ya faru.
Lamarin ya bayyana ne bayan mai riƙonta ya lura da sauyi a halayyarta sannan ya tambaye ta abin da ya faru.
Daga bisani an kai wadda abin ya shafa asibiti domin duba lafiyarta, inda sakamakon gwaji ya tabbatar da cewa an yi mata fyaɗe.
SP Nansel, ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin yayin da ake masa tambayoyi, sannan ya roƙi a yi mas sassauci.
Ya ƙara da cewa Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Shetima Jauro Mohammed, ya bayar da umarnin a miƙa lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar da ke Lafia domin zurfafa bincike, sannan daga bisani a gurfanar da shi a kotu.
Kwamishinan, ya tabbatar da cewa za a tabbatar da adalci, tare da gargaɗin jama’a da su yi taka-tsantsan da wuraren ibadar da suke zuwa da kuma mutanen da ke kiran kansu malamai ko fastoci.