An kama fasto mai garkuwa da mutane
Ya aika da wasikar barazana tare da kira domin ji ko an biya kudin fansa
Dubun wani fasto da ke garkuwa da mutane ta cika a Jihar Adamawa.
Kotun Majistare ta jihar ta sa a tsare faston a gidan yari bayan ya amsa tuhumar da ake masa na yunkurin garkuwa da wani magidanci.
- Bambamcin Ilimin ’Ya’ya Mata A Da Da Yanzu
- ’Yan Kwankwasiya sun far min da wuka, sun kwace wayata —Hadimin Ganduje
Fasto Joel Saul ya amsa laifin ne bayan dan sanda mai gabatar da kara, ASP Ezra Bulus, ya karanta masa tuhumar da ake masa na yunkurin yin garkuwa da mutane a gaban Alkali Alheri Ishaku.
ASP Ezra Bulus ya shaida wa kotun cewa Fasto Joel ya yi yunkurin yin garkuwa da wani magidanci a kauyen Mangere da ke kan hanyar Numan saboda mutumin ya ki ba shi Naira miliyan daya.
Ya kuma yi wa mutumin barazanar cewa kada ya kuskura ya bar gidansa sannan ya rika kira ya ji ko an biya kudin fansar.
Daga baya jami’an tsaro suka bibiyi lambar da ya yi amfani da ita wajen kiran mutumin har aka gano shi.
Bayan wanda ake zargin ya amsa laifin, ASP Ezra ya bukaci kotun ta dage shari’ar don ’yan sanda su samu ji daga Sashen Gabatar da Kara na Gwamnatin Jihar Adamawa.
Daga nan alkalin ya amince da hakan sanna ya ba da umarnin tsare faston a gidan yari.