An kama fasto ya yi wa ’yar shekara 12 fyade a coci
’Yar shekara 12 ta haihu bayan fasto ya yi mata fyade a coci
’Yan sanda sun cafke wani fasto mai shekara 48 kan zargin yi wa wata yarinya mai shekara 12 fyade a cocinsa, har ta dauki ciki.
Yarinyar, da ake zargin limamin cocin mai suna Fasto Micheal Abiodun, ya yi wa fyade, ’yar aji biyu na karamar sakandare ce, kuma tana zuwa ibada ne a cocinsa ne da ke Jihar Ogun.
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane a masallacin Juma’a a Zamfara
- Ana fakewa da barace-barace wajen aikata miyagun laifuka —Hisbah
Kakakin ’yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya ce a ranar Alhamis ne aka damke “Faston, wanda limami ne a cocoin The LightHouse Gospel Church”, da ke Oluwo, Owode Egba, Karamar Hukumar Obafemi Owode.
Ya ce an tsare wanda ake zargin ne bayan mahaifiyar yarinyar ta yi karar sa a Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Owode Egba.
Oyeyemi ya ce mahaifiyar yarinyar da faston ya dirka wa ciki ta ce ta fara zuwa cocinsa ne domin neman mafita daga wata matsala da ta yi sanadin mutuwar ’ya’yanta mata biyu.
“A ranar, faston ya umarci mahaifiyar yarinyar ta turo mishi ita ya yi mata addu’a ta musamman.
“Amma da yarinyar ta je, sai ya kai ta dakinsa da ke harabar cocin ya yi lalata da ita, wanda ya yi sanadiyyar daukar cikin,” in ji Oyeyemi, yana labarto abin da mahaifiyar yarinyar ta shaida musu.
Ya ce bayan korafin ne DPO ne Owode Egba, CSP Olasunkanmi Popoola, ya tura jami’ai suka je suka taso keyar faston.
“Da aka bincike shi, ya amsa cewa ya aikata laifin, amma ya ce sharrin shaidan ne.
“Ya kuma masa cewa shi ne ya fara lalata yarinyar wadda ke aji biyu na karamar sakandare.
“Mahaifiyar yarinyar ta bayyana cewa kasancewar ’yar tata ba ta fara jinin al’ada ba, shi ya sa ba ta iya lura tana da juna biyu ba, sai da ya kai wata bakwai,” a cewar Oyeyemi.
Ya kara da cewa yarinyar ta haihu mako uku da suka gabata kuma ta shaida wa ’yan sanda cewa ta kasa fada wa mahaifiyarta abin da ya faru ne saboda limamin cocin ya yi tsorata ta cewa mugun abu zai same ta idan kuskura ta fada wa wani abin da ya faru.
Rundunar ’yan sandan jihar ta tura kes din zuwa sashen binciken manyan laifuka gabanin gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.